Miliyoyin mahajjata sun yi jifar sheɗan yayin da aikin hajjin bana ke ƙarewa

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

A yayin da al’umma ke gudanar da hutun Babbar Sallah, mahajjata a Saudiyya sun yi jifar sheɗan a ranar Juma’a wanda ɗaya ne daga cikin wajiban ƙarshe a aikin hajjin.

Kimanin sama da mutane miliyan 1.6 ne suka yi jifar a duwatsu guda uku da ke nuni da tambarin sheɗan a Mina dake wajen birnin Makkah.

Tun da asubahin ranar ne mahajjata suka fara jifar domin samun sauƙi daga halin tsananin zafin rana da ƙasar ta ke da shi.

Jifan, aiki ne na koyi ne da Annabi Ibrahim (AS), a lokacin da sheɗan ya yi yunƙurin hana shi bin umarnin Allah na ya yanka ɗansa.

Wasu daga cikin mahajjatan sun bayyana yadda ibadar jifar ta zo musu da sauƙi inda suka riƙa kammalawa cikin ƴan lokuta.

Haka kuma wasu da dama sun hawu kan dutsen, wanda ake kira da ‘Jamrat’ duk da halin tsananin zafi da ƙasar take fama da shi da kuma gargaɗin zama a masauƙi daga ƙarfe 10 na safe zuwa 4 na yamma.

By Babaji