
Daga BELLO A. BABAJI
Shaguna da dama sun ƙone a yayin da gobara ta kama a kasuwar waya ta Farm Centre dake Jihar Kano.
Lamarin ya auku ne a safiyar ranar babbar sallah, wanda aka gano a lokacin da wani mutum ya yaɗa bidiyon a shafukan sada zumunta, inda aka ga hayaƙi na tsahi daga wani sashi na kasuwar.
Duk da cewa ba a kai ga sanin haƙiƙanin aukuwar lamarin ba, wani shaida ya ce gobarar ta ƙone shagunan da ke sayar da wayoyi ne da na kayayyakinsu.
Hukumar kashe gobara ta jihar ba ta fitar da wani jawabi ba game da lamarin a lokacin haɗa wannan rahoton.
Wani ƙaramin ɗan kasuwa mai suna Muhammad Daula ya faɗa wa manema labarai cewa da dama daga ciki masu shagunan ba sa nan a lokacin da abin ya faru ba duba da cewa sun shagal da hidindimun sallah.
Ya kuma ce, bidiyon da aka yaɗa ne ya tsinkayar da su cewa kasuwar ta kama da wuta.
