Daga ALI ABUBAKAR SADIQ
Wannan tambaya ce da aka daɗe ana yin ta tsawon tarihi, musamman daga mulhidai da ma wasu masu imanin, abinda ya sa Allah cikin ƙur’ani ya saukar mana da “Lam ya lid, wa lam yulad”, wato bai haifa ba, kuma ba a haife shi ba.
Kafin nan muna iya tunawa da Lamarudu, kamar yadda labarin ya zo cikin Bible da ƙur’ani, yadda ya ƙalubalanci Annabi Ibrahim (AS) cewa, shi ma Allah ne matuƙar cewa siffar Allah ta azurtawa da rayawa ce, to shi ma yana azurtawa da rayawa, yadda ya azurta wani talaka kuma ya saka aka saki wanda aka yanke wa hukuncin kisa. Kafin Ibrahima ya ƙure shi da cewa, to Allah ke fito da rana daga gabas ta faɗi a yamma.
A wannan zamani namu, akwai manyan mulhidai, irinsu Dawkins da Kraus da ma wasu yaranmu a nan Arewacin Nijeriya da ke inkarin samuwar Allah, sai suke irin wannan tambaya cewa, wane ne ya halicci Allah kansa. A yanzu mulhidai na amfani da kimiyyar zamani a matsayin makamin da za su ruɗar da mutane, kuma abin takaici yaƙin nasu na yin nasara sannu-sannu.
Ba nufina ba ne, na kawar da mulhidai daga aƙidarsu, sai dai haska wa matasa su gane wannan illar.
Kamar yadda kakanmu Annabi Ibrahim (AS) ya ke amfani da basira da nassi wajen wa’azi, ta haka ne kawai za mu iya murƙushe wannan annoba. Don haka muna da hanyoyi uku da za mu iya nuna wofintar tambayar cewa, wa ya halicci ubangiji. Wato ta hanyoyin hikima, falsafa da kimiyya.
A hankalce, idan za mu ɗauki misalin cewa, yaro ya yi fitsari a wandonsa, wandon zai jiƙe kuma idan ka taɓa wandon za ka ji danshi ko? Idan ka tambayi daga ina aka sami danshin, za a ce maka daga fitsarin ne. Shi kuma fitsarin daga ruwan da yaron ya sha, ka ga danshi ya dogara ne daga ruwa ko? Amma za ka iya tambayar cewa, daga ina shi kuma ruwan ya sami danshinsa? Ko kaɗan, domin danshin ba siffar ruwa ba ce, halayya ce. Tamkar haka ya sa ba za ka iya cewa wane ne ya halicci Allah ba, domin shi kaɗai ne ya iya ƙirƙirar halitta kuma ya tsara halitta yadda idan ba shi ba, babu wanda zai iya halittawa.
Idan akwai mai inkarin haka, sai Allah ya ƙalubalance shi a ƙur’ani da cewa:
ƙ22:73 “”Ya ku mutãne! ga wani misãli, sai ku saurãra zuwa gare shi. Lallai ne waɗanda kuke kira baicin Allah, bã zã su halitta ƙuda ba, ko da sun taru (gabaɗayansu) gare shi.”
Idan ka ce akwai mai halitta ba Allah ba, to kawo shi ya halicci ‘Kuda” kawai. Babu mai iya yin haka daga nan har tashin kiyama saboda Allah kadai ke iya halitta ba mai iya halitta wani abu ballantana ya halicci mai halittawa.
A kimiyance, idan muka duba za mu ga cewa ƙwayar halittar gado, wato DNA, idan da za a ce tsautsayi zai iya samar da guda ɗaya wanda sinadirai 2000 (enzymes) ne suke harhaɗuwa bisa wani tsari mai oda, to kafin tsautsayi ya iya haɗa su yadda Allah ya jera su sau ɗaya sai an gwada sau adadin 100000000000000000000000000000000000000000. Wannan adadi (sifili 40) ba shi da suna sai dai mu kira shi malala malala (malala gashin tinkiya, kamar yadda Bahaushe kan ce), domin ba gashin tinkiya ba, hatta ƙwayar tsakuwa, ɗigon ruwa, taurari da dabakoki kaf ba su kai wannan adadi ba.
Shi ya sa ba na mamakin ganin yadda tsawon dubban shekaru ɗan adam ya kasa gano sirrin rai. Masana kimiyya irinsu Francis Crick da Stanley Miller sun shafe gwamman shekaru a ɗakin gwajin kimiyya ko za su iya samar da ƙwayar halitta mai rai (cell), amma sun gaza ba tare da samar da abinda ya wuce sinadaran ‘Amino Acid’ ba, wato tubalin da ke gina ƙwayar halitta mai rai. Don haka ƙirƙirar halitta abu ne da babu wanda zai iya samar da ita sai Allah, mahaliccinta kuma kimiyya ta miƙa wuya.
Sannan mulhidai a wannan zamani sun ƙwace nazariyyar asalin halitta (eɓolution) tare da yi mata kwaskwarima yadda za ta nuna cewa, ai babu wanda ya yi halitta, wato halitta ta samar da kanta ne. Amma abinda mutane ba su sani ba shine cewa, shi wanda ake alaƙantawa da nazariyyar, wato Charles Darwin, ba mulhidi ba ne kuma har ya mutu ya yarda da Allah, abinda ya bayyana ƙarara cikin littafin tarihin rayuwarsa mai suna “Life and Letters”. Kuma ko a cikin gagarumin littafinsa wanda ya wallafa bincikensa “On the origin of species” bai taɓo asalin samuwar halitta ba, sai dai daga bayan samuwarta yadda ta wanzu a doron ƙasa kuma ta yaɗu. Amma bayan mutuwarsa, mulhidai sun ɗauki nazariyyarsa suke nuna cewa halitta ba wanda ya yi ta, ta samar da kanta ne da kanta.
Wani masanin kimiyya, Fred Hoyle, a shekarar 1952, ya gano wani tsarin daidaito a ƙwayar zarra ta ‘carbon’ (wadda ita ce ginshiƙin wanzuwar jikuna masu rai). Wannan ƙwayar zara na da wani daidaito, wanda ke nuna cewa idan da daidaiton ya gaza da kashi 4% kacal, to da duk ƙwayoyin zarra na ‘carbon’ ba za su samu ba. Kun ga da mu kanmu ba mu samu ba kenan. Wannan bincike ya sa masana tsunduma cikin wannan fage, ilai kuwa sai ga shi sun gano wasu tsarukan na daidaito (abinda ake kira da ‘Anthropic Principle’).
Tashin farko ita kanta ‘Big Bang’, wato haihuwar wannan sammai da ƙassai tamu (wadda Allah ya yi mana bayani a Suratul Anbiya aya ta 30) an gano cewa, da a daƙiƙa guda bayan fashewar, da a ce saurin faɗaɗar sammai ya gaza da kaso guda cikin wata lambar mai malala-malala (wato 1 da sifili guda sittin a bayanta) da samman ta koma ta sake dunƙulewa. Haka nan akwai ginshiƙan dokoki huɗu (Fundamental Forces), waɗanda ke ɗauke da duk wata halitta, walau mai rai ko mara rai;
1. Nukiliya mai ƙarfi (strong nuclear force), wacce ita ce ta ke zaunar da ’ya’yan ƙwayar zarra a dunƙule cikin tsakiyar ƙwayar zarra, wato ‘atom’ (ƙwayar zarra kuma ita ce tubalin ginin kowane irin jiki, mai rai da maras rai).
2. Nukiliya mai rauni (weak nuclear force), wacce ita ce ke saka ruɓewa (radioactiɓe) ta ƙwayar zarra.
3. Lantar-maganadisu (electromagnetism), wacce ita ce ginshiƙin sufuri na lantarki da maganɗisu da ke ɗaukar haske, kuzari da su radiyo, ɗ-ray, infrared, microwaɓe da sauransu.
4. Maganaɗisu (graɓity) wacce ita ce motsin jiki kama daga manyan ɗabakoki, taurari da duniyoyi da abinda ke cikinsu har zuwa kan ƙwayar zarra.
Duk waɗannan dokokin, Allah ya saita kowanne iya wani geji wanda a misali Idan da a ce nukiliya mai karfi ZAI yi rauni daga gejinsa, to da babu wata ƙwayar zarra banda ta ‘Hydrogen’ da za ta iya samuwa. Idan kuma da nukiliya mai rauni ƙarfinsa ya wuce yadda ya ke, to da duk ‘Hydrogen’ ta zama ‘Helium’. Haka nan shi ma Lantar-maganaɗisu da ƙarfinsa ya fi yadda ya ke, to da duk ƙwayoyin zarra za su dunƙule yadda ba za su iya ta’ammali da wasu ƙwayoyin zarra wajen auratayya, domin samar da wasu gungun sinadarai ba. Da kuma ƙarfin Lantar-maganaɗisu ya gaza yadda ya ke, haƙiƙa da ƙwayoyin zarra sai su yi ta ruɓewa. Yanzu wannan tsarin ne za ka ce katsam ya samu babu wanda ya samar da shi?
Mulhidanci, addinin shaiɗan ne da ke ƙoƙarin yin amfani da kimiyya ta ƙarya (‘Pseudo-science’), domin dulmuyar da matasanmu. Sun cusa abin cikin hikima da wayo ta yadda suka mamaye ɓangarorin nazariyyar kimiyya da nazarinta, inda suka ɗauki wancan bincike na Darwin akan asalin halitta suka kafirtar da shi. Haƙiƙa sun kafirtar da shi ne, domin sama da shekaru 600 kafin Darwin, malaman Musulunci fitattu guda uku sune suka fara gano yadda tsarin yake sakamakon umarnin Allah da ya ce;
ƙ29:20 “Ka ce: ‘’Ku yi tafiya cikin ƙasa, sa’an nan ku dũba yadda (Allah) Ya fãra yin halitta’.”
Don haka Al Haytham cikin littafinsa “Kitabul Manazir” da Al Biruni cikin littafinsa “Kitabul Jamahir” da kuma Ibn Khaldun a nasa littafin “Al Muƙaddima”, duk sun kawo nazariyar asalin halitta. Amma barcin da Musulmi suka yi da daina binciken ilimi, sai Turawa suka sace ilimi gabaɗaya.
Bayan Darwin ya buga tasa nazariyyar, sai wasu mulhidai ƙarƙashin jagorancin Thomas Huɗley su ka karkata akalar binciken da lulluɓe shi cikin mulhidanci tare da kwaikwayar tsarin addini a fakaice, inda suka maida nazariyyar tamkar Bible ɗinsu, tare da ɗauke duk wani ‘ƙuality’ (inganci) na ubangiji suka mayar wa “nature” tare da samar da mujalla mai suna ‘Nature’ ta zama kakakinsu. Sun maida jami’o’i tamkar masallatansu, inda suke ɗaukar malaman kimiyya, domin koyar da mulhidanci da sunan kimiyya. An fitar da tsarin wallafa bincike (peer reɓiew) yadda ya zama tsarinsu na wa’azi yadda sai wanda suka aminta da shi zai samu sahalewar a buga bincikensa kuma a yaɗa shi. Ta haka ake samar da mabiya sabbi sannan manyan annabawansu su ne irinsu Dawkins da Krauss da ke kira zuwa ga addinin ta hanyar wa’azi a littafansu da lakcoci.
A bayyane ya ke cewa ɗan adam ya gaza wajen ganowa ta hanyar kimiyya ina halitta ta samo asali kuma ina rai ya sami asali. Hatta hankali na gane abubuwa (consciousness) da ni da kai da kowa ke da shi, babu wanda ya san asalinsa. Haka nan a kullum kimiyya dada tabbatar da mahalicci ta ke yi a cikin tsarin halitta. Kafin bayyanar Einstein, sakamakon nazariyyar Darwin da yadda aka lullube ta da mulhidanci hadi da nazariyyar Isaac Newton wanda ya kawo dokokin motsin jikuna (Laws of motion) a karshen karni na 19 sai masana kimiyya masu ra’ayi na mulhidanci suka daga hannu da shewar cewa an ga bayan addini, yadda gagarumin mulhidi dan Jamus Freidrich Nietzsche ya wallafa littafinsa “The Death of God” wato kimiyya ta kashe Allah ba shi da sauran tasiri domin komai a yanzu kimiyya zata iya bayaninsa.
Katsam sai Allah ya jefo Einstein, wanda nazariyyarsa ta ‘Relatiɓity’ ta zo ta yi rugu-rugu da tsarin “Reductionism” cewar kimiyya za ta iya bayyana komai. Sai aka gane cewa komai “dan ya danganta ne” da wani abu (wato Relatiɓe), wanda kuma ya haɗe sarari (space) da lokaci (time) cewa a dunƙule suke ba daban-daban ba.. Wannan mahanga ta dawo da samuwar Allah cikin tsara halitta, sannan ta ƙarfafa bayan samun nazariyyar Werner Heisenberg wanda ya gano sabuwar dokar da aka kira da “Uncertainty principle”, wato dokar “ƙila-wa-ƙala” a kimiyya, dokar da hatta shi gwarzon kimiyyar ɗan adam, wato Einstein da kansa, bayan nazarin dokar yadda ta ke, sai da ya shiga ruɗanin da ya ce “God does not play dice” (wato “Kai, a ce Allah zai yi wasan dara?).
Domin abin da dokar ƙila-wa-ƙala ta gano shine cewa, idan ka yi ƙoƙarin auna inda ’ya’yan ƙwayar halitta (wato ‘particle’) su ke to, ba kuma za ka iya auna gudunsu ba a lokaci guda. Idan kuma ka iya auna gudun, to haƙiƙa inda su ke zai kauce maka. Babu wato doka a kimiyya da ta tabbatu a zahirance irinta, domin ba giɓin iliminmu ne ya sa hakan ba, illa dai yadda Allah ya tsara halittar. Wannan doka (ƙuantum indeterminacy) a yanzu ana amfani da ita wajen ƙere-ƙeren kwamfuta masu tsananin gudu da sauran abubuwa.
Ya ilahi, idan har ba ka iya gane yaya halitta maras rai ta samu ba, ko yadda rai ya samu, ko kuma ina hankalin gane abubuwa (consciousness) ya me, da hatta yadda tsarin ƙwayoyin halitta mafi ƙanƙanta ke wanzuwa… shine kuma za ka fara giggiwar wai wa ya halicci Allah?
Mulhidai ku ci gaba da wasa ƙwaƙwalenku a waɗannan abubuwa tukuna kafin gu gaza, domin kimiyya duk ta rufe ƙofofinsu. Shi wanda kuke inkari shine;
Q6:103 “(Ubangijinku shine wanda) Gannai ba su iya riskuwarSa, kuma Shi Yana riskuwar gannai, kuma Shi ne Mai tausasãwa, Masani”.
A ƙarshe, ƙalubalenku malamai, dole ku farka daga barcinku domin cika nauyin da ke kanku. Ilimin kimiyya da falsafa wajibi ne kamar yadda mu ka gani Allah na ta umartarmu a ƙur’ani, sannan mun ga yadda ta hanyar falsafanci Ibrahimu (AS) ya wofintar da Lamarudu akan magànar wane ne Allah. Kuma kada mu manta Annabi ya umarce mu da cewa, “Hikima kayanmu ce, duk inda muka gan ta mu ɗauki abarmu”.
Amma kash! Malamai sun shagala da duniya sai neman arziki da neman girma da kwaɗayi da faɗa da juna akan abubuwa marasa mahimmanci. Malamai sun gidadantar da wayayyen addini, saboda ƙyamatar nazari da bincike, sun ɓige da rigima akan mabambantan fatawoyi da ɓangarancin ƙungiya. Wannan dalili ya sa matasa a Arewa ke zama mulhidai, domin malamai ba sa iya ba su amsoshin da ke musu yawo a ƙwaƙwalwarsu, saboda su kansu malaman sun jahilci al’amuran. Haka nan tsattsauran ra’ayin addini shi ma ya yi tasiri sosai wajen kore matasa daga addini.
Barkanmu da Juma’a!
Malam Ali manazarci ne kuma masani a Jihar Kano
