Amurka za ta wanke waɗanda aka ɗaure kan kisan Malcolm X

Hukumomin Amurka na shirin wanke wasu mutane biyu da aka samu da laifin kashe fitaccen mai kare haƙƙin Bil Adama Malcolm X a shekarar 1965 saboda abinda suka kira kuskure wajen yi musu shari’a.

Ana sa ran yau Babban lauyan Manhattan, Cyrus Vance ya jagoranci taron manema labarai inda zai sanar da wanke mutanen biyu Muhammad A. Aziz da Khalil Islam.

An ɗaure Aziz mai shekaru 83 ɗaurin rai da rai a shekarar 1966, amma kuma sai aka sake shi a shekarar 1985, yayin da aka saki Islam a shekarar 1987, ya kuma rasu a shekarar 2009.

Vance ya ce ba a yi wa mutanen biyu adalci ba lokacin da aka mu su shari’a aka kuma ɗaure su, saboda haka ya dace su amsa kuskuren da suka yi wajen shari’ar.

Jaridar New York Times ta ruwaito cewar bayan wani sabon bincike na watanni 22 da aka gudanar, ofishin Babban lauyan gwamnati da lauyoyin mutanen biyu sun gano cewar ma su gabatar da ƙara da hukumar FBI da kuma ofishin ‘Yan Sandan New York sun ɓoye shaidun da ke iya wanke mutanen biyu lokacin da aka mu su shari’ar.

Wani mutum na 3 da aka tuhuma da kisan, Mujahid Abdul Halim mai shekaru 80 ya amsa kashe Malcolm X, kuma ya shaida wa kotu cewar, Aziz da Islam ba su da hannu wajen aikata kisan da aka yi ranar 21 ga watan Fabarairun shekarar 1965 lokacin da Malcolm X ke shirin gabatar da jawabin sa a Manhattan, amma sai ma su gabatar da ƙara suka ɓoye shaidar.

Wannan shari’a ta ɗauke hankalin mutanen ciki da wajen Amurka, waɗanda suke bayyana damuwa akan rashin adalcin da aka yi wa mutanen biyu na shekaru 56.