Dokar hana ganin Fursunoni na ci gaba da aiki a Togo

Hukumomi a Ƙasar Togo sun haramtawa dangi da ‘yan’uwan fursunoni da ke gidajen yari a faɗin ƙasar kai duk wata ziyara don saduwa da fursunoni da ke zaman kaso.

Watanni 18 kenan da aka kafa wannan doka don a yaƙi cutar Korona daga kama shiga gidajen yari.

Mutane da yawa daga cikin dangi da ‘yan’uwan fursunoni da ke gidan kaso sun koka matuqa saboda wannan mataki da ke hana su ganin mutanensu.

Ministan Sharia na ƙasar Pius Agbetomey, tun a bara ya sanar da cewa an hana kai ziyara gidajen yari da ke faɗin ƙasar har sai illamasha’a saboda annobar cutar Korona.

Yanzu haka akwai mutane 26,167 da aka gano sun harbu da ƙwayar cutar Korona.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *