Daga MUHAMMADU MUJITTABA a Kano
An ƙaddamar da kwamitin buɗe Cibiyar Gidauniyar Salihannur, wacce za ta tallafa wa kimanin mutane 1,000 a fannoni daban-daban. An ƙaddamar da kwamitin ne a wani taro da aka gudanar a Gidan Mumbayya da ke Kano.
Shugaban gidauniyar, Dakta Adam Salihu (Salihannur), ya bayyana cewa cibiyar ta ƙunshi sassa uku: sashen kula da masu buƙata ta musamman, makarantar koyon ilimin magunguna, da kuma sashen bayar da magunguna.
Ya ce za a tallafa wa masu naƙasa 300, marasa lafiya masu hawan jini, suga da daji 300 da magani kyauta, marayu 100 da aka koyar da sana’ar takalma, matasa 150 da aka horas da magungunan gargajiya, da teloli 100 da aka koyar da dinki na zamani.
Shugaban kwamitin buɗe cibiyar, Abdusalam Mu’azu Nayaya, ya ce kwamitin zai yi aiki tukuru domin tabbatar da nasarar shirin, la’akari da muhimmancin lokaci da bukatar al’umma.
