Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Jama’a, Mohammed Idris, ya ce Nijeriya ta warware rikicin diflomasiyya da ya taso tsakaninta da Amurka, lamarin da ya ƙara ƙarfafa dangantakar ƙasashen biyu.
Idris ya bayyana hakan ne a Abuja yayin taron manema labarai na ƙarshen shekara, inda ya ce an cimma matsaya ne ta hanyar tattaunawa mai ƙarfi da mutunta juna.
Ya ce yarjejeniyar haɗin gwiwar kiwon lafiya ta shekaru biyar da darajar dala biliyan 5.1 da aka kulla tsakanin ƙasashen biyu shaida ce ta ƙarfafa alaƙar.
A cewarsa, yarjejeniyar za ta ƙarfafa tsarin kiwon lafiyar Nijeriya , ta ceci rayuka tare da jawo zuba jari.
Idris ya ƙara da cewa Nijeriya ta bayyana a matsayin ƙwararriyar abokiyar hulɗa a fagen duniya, tana kare muradunta tare da gina haɗin gwiwa masu amfani.
Dangantakar Nijeriya da Amurka ta fuskanci ƙalubale a wannan shekara bayan Amurka ta rage bada biza ga ’yan Nijeriya , ta ayyana ƙasar a matsayin “ƙasa mai damuwa ta musamman” tare da sanya wasu takunkumai da ƙuntatawar tafiye-tafiye.
Duk da haka, gwamnati ta ce tattaunawa ta diflomasiyya ta kai ga daidaita rikicin da ƙarfafa alaƙar da ke tsakanin ƙasashen biyu.
