Man da ake samarwa a kullum ya kai lita miliyan 71.5 – NMDPRA

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Hukumar kula da harkokin sarrafawa da tacewa da sufurin man fetur a Nijeriya, NMDPRA ta bayyana cewa yawan man fetur da ake samarwa a kullum ya ƙaru zuwa lita miliyan 71.5 a watan Nuwamba 2025, daga lita miliyan 46 a kullum da ake samu a watan Oktoba.

Hukumar ta ce gagarumin ƙarin a watan Nuwamba ya samo asali ne daga shigo da man da Kamfanin NNPCL ya yi, wanda ya samar da kashi 55 cikin 100 na wadataccen man fetur a kasuwannin Nijeriya, daga hanyoyin cikin gida da kuma ƙasashen waje.

Takardar bayanai ta watan Nuwamba 2025 da aka fitar a ranar Litinin ta nuna cewa yawan amfani da man fetur a ƙasar ya ƙaru da kashi 44.5 cikin 100 zuwa lita miliyan 52.1 a kullum a watan Nuwamba, idan aka kwatanta da lita miliyan 28.9 a watan Oktoba, lamarin da ya nuna akwai ƙarin lita miliyan 37.4.

A cewar rahoton, matatun mai na cikin gida sun samar da lita miliyan 17.1 a kullum a wannan lokaci, yayin da matsakaicin yawan amfani da man fetur a watan ya kai lita miliyan 52.9 a kullum.

Sai dai NMDPRA ta bayyana cewa ba a samar da mai daga dukkan matatun mai na gwamnati da suka haɗa da na Fatakwal da Warri da Kaduna, domin matatun sun ci gaba da kasancewa a rufe.

By ukarofi