Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Jama’a, Mohammed Idris, ya ce, gwamnatin tarayya ta shirya kakkaɓe ‘yan ta’adda daga dazukan Nijeriya.
Idris ya bayyana hakan ne a yayin gana wa da manema labarai na ƙarshen shekara a Abuja a ranar Litinin.
Ya yi bayanin cewa, shugaban ƙasa ya bayyana dokar ta-ɓaci a kan tsaro a ƙasa baki ɗaya a shekarar 2025 da muke bankwana da ita.
A cewarsa, wannan dokar ta-ɓaci za a ga amfaninsa a watanni masu zuwa musamman ɗaukar sabbin sojoji da jami’an ‘yan sanda.
“Kuma za a tura jami’an tsaron dazuka waɗanda aka za su kiyaye dazuka da sauran wurare masu rauni.”
“Akwai wasu wurare masu haɗari a dazukanmu waɗanda babu jami’an tsaro a wurin wanda ke bai wa ‘yan ta’adda damar sakewa su ci karensu ba babbaka.
“Da wannan ɗaukar ma’aikata da ayyana dokar ta-ɓaci da shugaban ƙasa ya ba da umarni, ba wani wuri da ‘yan ta’adda za su samu su ɓuya a dazukanmu.
“Sannan a 2025 mun samar da sabon tsarin yaki da ta’addanci waɗanda za a yi amfani da abubuwa 4 da suka haɗa da: Dunƙulallen tsarin ba da umarni da tattara bayanan sirri da daidaita al’amura a garuruwa da mayar da martani,” Idris ya faɗa.
Ya kuma ƙara da cewa a shekarar 2025, an yi nasarar kama gawurtaccen ɗan ta’adda kuma shugaban ISWAP da ke zaune a Nijeriya ta hanyar haɗin kan jami’an tsaro. Kuma ana dab da gabatar da shi a gaban kotu.
“Bari na yi ƙarin haske kan cewa daga yanzu duk wasu gungun ‘yan ta’adda da suka yi garkuwa da ‘ya’yanmu ko suka kai wa manoma hari ko suka farmaki mutanen gari, to a ayyana su ne a matsayin ƙungiyar ‘yan ta’addanci.”
“Lokacin yin zame-zame wajen kiran gauta ja ne, ya wuce,” inji Idris.
