An ƙaddamar da littafin rayuwar Marigayi Salisu Mu’azu Kiru 

Spread the love

Daga SULEIMAN HUSSAINI D/KUDU a Kano

A ranar Lahadin da ta gabata ne aka kaddamar da littafin da ya ƙunshi tarihin rayuwar fitaccen ɗan gwagwarmayar siyasa, Marigayi Salisu Mu’azu ƙiru, wanda aka fi sani da Salisu Shugaba – ɗan Mazanjiya. 

Taron ƙaddamarwar ya samu halartar manyan ‘yan siyasa, ‘yan kasuwa, malamai, sarakunan gargajiya, ‘yan uwa da abokan arziki, inda Kwamared Rabiu Lawan Gambo (Kwamared Dogo) ya wallafa littafin.

Shugaban taron kuma tsohon Sanatan Kano ta Kudu, Sanata Mas’ud El-Jibrin Doguwa, ya bayyana taron a matsayin rana mai cike da tarihi wadda ba za a manta da ita ba. Ya ce marigayi Salisu Mu’azu Kiru ya bayar da gagarumar gudunmawa ga al’umma wadda tarihi ba zai manta da ita ba, ba a garin Kiru kawai ba, har ma da Jihar Kano da ƙasa baki ɗaya.

Sanata Doguwa ya bayyana marigayin a matsayin mutum mai kishin ci gaban al’umma, mai ƙarfafa zumunci da haɗin kai, tare da jajircewa wajen magance matsalolin jama’a domin samar da ci gaba. Ya ce taron ya kasance wata hanya ta tunawa da ayyukan alheri da gudunmawar da marigayin ya bayar a lokacin rayuwarsa domin ya zama abin koyi ga masu tasowa.

A nasa jawabin, babban mai ƙaddamar da littafin kuma Sanata mai wakiltar Kano ta Kudu a Majalisar Dattawan Nijeriya, Sanata Abdurrahman Kawu Sumaila, ya bayyana rayuwar marigayi Salisu Mu’azu Kiru a matsayin abin koyi da ya kamata al’umma su yi koyi da halayensa da dabi’unsa. Ya ce marigayin ya taka muhimmiyar rawa wajen bunƙasa yankinsa ta fannoni da dama, musamman wajen taimakon jama’a da haɗa kan al’umma.

Sanata Sumaila ya ƙara da cewa irin jajircewar da marigayin ya nuna wajen tallafa wa al’umma da samar da ci gaba ya haifar da gagarumin sauyi, wanda tasirinsa ya wuce iyakokin garin Kiru zuwa Jihar Kano da ma ƙasa baki ɗaya.

Da yake bayani kan dalilin rubuta littafin, marubucin littafin Kwamared Rabiu Lawan Gambo ya ce abin da ya ba shi sha’awar rubuta littafin shi ne irin rawar da marigayin ya taka wajen samar da ayyukan ci gaba ga al’ummar yankinsa, ciki har da taimaka wa matasa samun mukamai a gwamnatocin jiha da tarayya, da kuma ƙoƙarinsa wajen haɗa kan al’ummar Kano ta Kudu duk da bambancin jam’iyyu.

Marubucin ya bayyana cewa littafin ya kunshi cikakken tarihin rayuwar marigayin da gudunmawar da ya bayar a fannoni daban-daban da suka haɗa da kasuwanci, siyasa, ilimi, addini, sarauta da harkokin gwamnati. Ya ce littafin ya kuma haskaka irin rayuwar da marigayin ya yi mai cike da jajircewa, gaskiya da kishin al’umma.

Ya ƙara da cewa babban manufar littafin ita ce adana tarihin rayuwar marigayin wanda ya taka muhimmiyar rawa wajen gina ci gaban Kiru tun daga zamanin mulkin mallaka har zuwa zamanin dimokuraɗiyya.

Littafin wanda aka yi wa lakabi da “Littafin Mazanjiya” ya kuma bayyana asalin marigayin tun daga tushe, ciki har da tarihinsa na iyali, yadda ya taso, neman ilimin addini da na boko, shigarsa harkokin kasuwanci da siyasa, har zuwa lokacin da ya zama shugaban jam’iyyar PRP a Kiru a shekarar 1979, sannan daga bisani ya wakilci yankin Kiru a Majalisar Dokokin Jihar Kano a shekarar 1983 kafin juyin mulkin soja.

Hakazalika, littafin ya ƙunshi darussa masu yawa ga al’umma musamman ‘yan siyasa, domin su fahimci muhimmancin gaskiya, riƙon amana da kishin al’umma wajen gina shugabanci nagari. Marubucin ya ce littafin zai taimaka wa manazarta tarihi da masu bincike, domin ya kunshi bayanai kan tarihin siyasar Nijeriya tun daga zamanin mulkin mallaka, mulkin soja da kuma dimokuraɗiyya.

Da yake jawabin godiya a madadin iyalan marigayin, Injiniya Sarki Aliyu Salisu ya nuna farin ciki da godiya ga marubucin littafin bisa wannan gagarumin aiki. Ya ce littafin ya zama wata muhimmiyar hanya ta adana tarihin rayuwar mahaifinsu.

Ya bayyana cewa marigayin mutum ne mai son ci gaban al’umma da ƙarfafa zumunci, yana mai cewa duk abin da ya samu, yakan yi amfani da shi ne wajen taimakon jama’a. Ya ƙara da cewa duk da cewa marigayin bai bar tarin dukiya ba, amma ya bar gadon ilimi da tarbiyya wanda iyalansa suka ginu a kai.

Mahalarta taron sun bayyana jin daɗinsu tare da yaba wa marubucin littafin, inda suka ce marigayin ya bar abin koyi ga al’umma, musamman ga matasa da shugabannin siyasa masu tasowa.

By ukarofi