Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Gwamnatin Nijeriya ta ƙaddamar da wani gagarumin rabon tallafin abinci da magunguna da abinci mai gina jiki a jihohin arewacin ƙasar 10 da ke fama da matsalolin jinƙai.
Yayin ƙaddamar da shirin Gwamnan jihar Sokoto, Ahmad Aliyu ya ce gwamnatin tarayya ta ɓullo da shirin domin tallafa wa al’umomin da ke fama da talauci a jihohin arewacin ƙasar 10.
Yayin da yake jawabi a garin Kasarawa, inda aka ƙaddamar da shirin, gwamnan ya ce shirin wanda shugaban ƙasar, Bola Tinubu ya ɓullo da shi, ya zo daidai da zuwan azumin watan Ramadan, lokacin da aka fi buƙatar tallafin.
Taron ƙaddamarwar ya samu halartar ministan ayyukan jin ƙai da kawar da talauci na ƙasa Dr. Yusuf Tanko Sununu.
Gwamnan ya ce ƙudirin shugaban ƙasar ya yi daidai da muradin gwamnatin jihar na raba wa mabuƙata tallafi.
Kimanin mutum 1,000 suka amfana da tallafin kamar yadda gwamnan ya bayyana.
”Haka a yanzu da watan Azumi ke gab da shigowa za mu raba buhunan masara da kuɗi naira 50,000 ga mutane 1,000 da suka ci gajiyar tallafin, da suka haɗa da mabuƙata da marayu da gajiyayyu da zawarawa da ‘yangudun hijira da tsofaffi daga gwamnatin tarayya domin sauƙaƙa musu azumin,” inji Gwamna Ahmad Aliyu.
Tallafin da aka raba ya haɗa da buhunan shinkafa da jarakunan manja da man gyaɗa da wasu nau’ikan abinci masu gina jiki.
Jihohi 10 da za su amfana da wannan tallafi sun haɗa da Borno da Adamawa da Yobe da Benue da Neja da Filato da Katsina da Zamfara da Sokoto da kuma jihar Kebbi.
