Yadda asibitoci da jami’o’i ke fama da tsadar lantarki duk da alƙawarin gwamnati

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Shirin Gwamnatin Tarayya na samar da ingantacciyar wutar lantarki ga jami’o’in Gwamnatin Tarayya da asibitocin koyarwa a faɗin Nijeriya ya samu babban tazgaro, bayan da aka kasa fitar da kuɗaɗen da aka ware wa aikin cikin Dokar Kasafin Kuɗin 2025.

Ko da yake an tanadi kimanin naira biliyan 300 domin wani shiri na musamman na inganta lantarki, wani binciken jaridar News Point ya nuna cewa har yanzu ba a fitar da ko sisi ba daga cikin kuɗaɗen, lamarin da ya sa ba a fara aiwatar da aikin ba duk da sanar da shi tun bara.

Mai bai wa Ministan Wutar Lantarki shawara kan harkokin yaɗa labarai, Bolaji Tunji, ya tabbatar da cewa aikin ya tsaya cak sakamakon rashin sakin kuɗaɗen kasafin. A cewarsa, babu wani cigaba da aka samu kan shirin tun da ba a samu kuɗin aiwatarwa ba.

An ƙirƙiro shirin ne domin magance matsalar yawan katsewar wuta a manyan cibiyoyin gwamnati, musamman asibitocin koyarwa da jami’o’i, waɗanda ke dogaro da janareto mai amfani da dizal domin tafiyar da ayyukansu na yau da kullum.

Tun farko Gwamnatin Tarayya ta bayyana aniyar girka tsarin hasken rana na haɗin gwiwa da sauran hanyoyin samar da makamashi mai sabuntawa, domin tabbatar da wutar da ba ta yankewa. Ana sa ran shirin zai rage kuɗaɗen tafiyar da ayyuka, ya ƙara inganta ayyukan kiwon lafiya da ilimi, tare da ƙarfafa amfani da makamashi.

Shugaban Kwamitin Kasafin Kuɗi na Majalisar Wakilai, Abubakar Bichi, ne ya bayyana ware kuɗin na biliyan 300 yayin ƙaddamar da aikin hasken rana a Asibitin Koyarwa na Aminu Kano da ke Kano. Ya ce matakin na daga cikin ƙoƙarin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na kawo ƙarshen matsalar katsewar wuta a muhimman ɓangarori.

Bichi ya ce an ɗauki matakin ne domin tabbatar da cewa asibitoci da jami’o’i sun samu wuta ba tare da tangarɗa ba, ta yadda likitoci za su iya ceton rayuka, ɗalibai kuma su yi karatu cikin kwanciyar hankali. Ya ƙara da cewa, Hukumar Makamashi ta ƙasa za ta haɗa gwiwa da hukumomin da abin ya shafa wajen tabbatar da aiwatar da shirin.

Daga cikin cibiyoyin da aka lissafa a matsayin masu cin gajiyar shirin akwai Asibitin Koyarwa na Aminu Kano, Jami’ar Bayero Kano, Asibitin Kwararru na Murtala Muhammad, Asibitin Nasarawa, Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ibadan, Jami’ar Ibadan, Jami’ar Legas, Jami’ar Obafemi Awolowo da ke Ile-Ife, Jami’ar Nijeriya da ke Nsukka da kuma Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya.

Sai dai kusan shekara guda bayan ware kuɗin, yawancin wazannan cibiyoyi ba su ga ko fara aikin ba. Jami’an hulɗa da jama’a na wasu daga cikin asibitocin sun tabbatar da cewa an sanya su cikin jerin sunayen masu cin gajiya, amma har yanzu ba a girka wani tsarin mini-grid ba.

Jinkirin na zuwa ne a daidai lokacin da farashin wutar lantarki ya karu bayan sauye-sauyen tsarin kuɗin fito, lamarin da ya ƙara nauyin kuɗi a kan asibitoci da jami’o’i. Duk da amincewar gwamnatin da bayar da tallafin kaso 50 cikin dari a watan Agustan 2024, har yanzu cibiyoyi da dama na kokawa da tsadar wuta.

Masana harkokin kasafin kuɗi sun bayyana cewa duk da ware kuɗaɗe a takarda, aiwatar da ayyuka na buƙatar ainihin sakin kudi daga Ma’aikatar Kuɗi da Ofishin Kasafin Kuɗi na Tarayya. Rashin hakan ne ya sa ayyuka da dama ke tsaya wa cik, duk da girman kasafin da ake amincewa da shi a kowace shekara.

A halin yanzu, masu ruwa da tsaki na nuna damuwa cewa idan ba a gaggauta sakin kuɗaɗen ba, shirin na biliyan 300 na iya zama a rubuce kawai, yayin da jami’o’i da asibitoci ke ci gaba da fama da matsalar katsewar wuta da tsadar dizal.

By ukarofi