Makarantu masu zaman kansu na tallafa wa gwamnati — Kwamared Alkanawy

Spread the love

Daga SULEIMAN HUSSAINI D/KUDU a Kano

Shugaban Sahal College of Health Science and Technology kuma shugaban ƙungiyar kwalejojin koyar da aikin lafiya masu zaman kansu ta Jihar Kano (Progressiɓe Forum of Priɓate Colleges of Health Science and Technology, Kano State Branch), Kwamared Muhammad Ibrahim Alkanawy, ya bayyana cewa makarantu masu zaman kansu na taka muhimmiyar rawa wajen tallafawa gwamnati, musamman a fannin horas da ma’aikatan lafiya da kuma rage matsalar rashin aikin yi ga matasa.

Kwamared Alkanawy ya bayyana hakan ne yayin wata ganawa da manema labarai a ofishinsa da ke harabar makarantar a Kano, makon da ya gabata. Ya ce makarantu masu zaman kansu suna rage nauyin da ke kan gwamnati wajen samar da ayyukan yi ga matasa, tare da cike giɓin da ake da shi a fannin ilimin kiwon lafiya.

Ya ƙara da cewa buɗe irin waɗannan makarantu ya kawo gagarumin ci gaba a fannin ilimi, musamman idan aka kwatanta da yadda al’amura suke a baya. A cewarsa, makarantu masu zaman kansu sun taimaka wajen wayar da kan al’umma da samar da ƙwararrun ma’aikatan lafiya da ake matuƙar buƙata a ƙasar nan.

Kwamared Alkanawy ya bayyana cewa babban dalilin buɗe makarantar shi ne ganin irin koma bayan da ake samu a fannin ilimi, musamman ilimin kiwon lafiya. Ya jaddada cewa ilimi shi ne ginshiƙin ci gaban al’umma, domin ta hanyarsa ne ake samun sauye-sauye masu amfani a rayuwar jama’a.

Ya yi kira ga gwamnatoci a matakai daban-daban da su riƙa shiga cikin harkokin makarantu masu zaman kansu ta hanyar kai ziyara domin duba yadda ake tafiyar da ayyukansu. Ya ce hakan zai taimaka wajen inganta harkokin ilimi da kuma shigar da irin waɗannan makarantu cikin shirye-shiryen gwamnati, ciki har da gyaran makarantu da sauran tallafi, wanda hakan zai taimaka wajen bunƙasa aikin su da rage rashin aikin yi tsakanin matasa.

Haka kuma ya ja hankalin iyaye da su riƙa sanya ido sosai kan yadda ‘ya’yansu ke tafiyar da karatunsu, domin samun nasarar da ake buƙata a rayuwarsu ta gaba.

Da yake magana kan ƙalubalen da makarantu masu zaman kansu ke fuskanta, Kwamared Alkanawy ya ce babban matsalar da suke fama da ita ita ce rashin fahimta daga wasu iyayen ɗalibai, musamman wajen cika alƙawarin biyan kuɗin makaranta. Ya bayyana cewa kuɗaɗen makaranta su ne ake amfani da su wajen biyan malamai, biyan kuɗin haya da kuma siyan kayan aikin gudanarwa.

Ya kuma ƙara da cewa makarantu masu zaman kansu na fuskantar ƙarancin kulawa da tallafi daga gwamnati, inda ya ce idan aka samar da irin wannan tallafi, hakan zai ƙara musu ƙwarin gwiwa wajen ci gaba da gudanar da ayyukansu.

Da yake bayani kan nasarorin da makarantar ta samu tun bayan kafuwarta, Kwamared Alkanawy ya ce makarantar ta fara ne da cibiyar horas da ilimin na’ura mai kwakwalwa (Computer Training Institute) a shekarar 2013, inda suka samu nasarar yaye ɗalibai kimanin dubu 20.

Ya ce daga bisani makarantar ta fara shirin share fagen shiga jami’a (Remedial Studies) a shekarar 2015, wanda ta samu nasarar yaye ɗalibai kimanin dubu biyar. Bayan haka, makarantar ta faɗaɗa ayyukanta zuwa fannin koyar da ilimin kiwon lafiya, inda zuwa yanzu ta yaye ɗalibai sama da 200.

Hakazalika, ya bayyana cewa makarantar ta samu nasarori da dama, ciki har da samar da dakunan gwaje-gwaje na zamani, kafa asibitin makarantar wanda ba ɗalibai kaɗai ke amfana da shi ba har ma da al’umma baki ɗaya, da kuma kafa cibiyar jarabawar shiga jami’o’i ta ƙasa (JAMB CBT Centre) wadda ke ɗaukar ɗalibai sama da 200 a lokaci guda.

Kwamared Alkanawy ya tabbatar da cewa makarantar za ta ci gaba da faɗaɗa ayyukanta domin samar da ƙwararrun ma’aikatan lafiya da za su taimaka wajen bunƙasa harkokin kiwon lafiya da ci gaban al’umma.

By ukarofi