Ribas: Fubara ya tsige kwamishinonin gwamnatinsa

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Gwamnan Jihar Ribas, Siminalayi Fubara ya sauke baki ɗaya ‘yan tawagar majalisar zartarwar gwamnatin jihar.

Sakataren watsa labaransa, Onwuka Nzeshi ya sanar da haka ga manema labarai a wata takarda, ranar Alhamis.

A cewar sanarwar, gwamnan ya umarci dukkan kwamishinoni da masu taimaka masa na musamman da su miƙa jagorancin ofisoshinsu ga manyan sakatarori ko manyan jami’an guraben da aka ba su.

Fubara ya kuma bayyana godiyarsa ga mambobin majalisar bisa hidimarsu ga harkokin gwamnatin da yi musu fatan alheri a al’amuransu na nan gaba.

Hakan na zuwa ne ƙasa da sa’o’i 48 da Ministan Abuja Nyesom Wike ya tabbatar da yunƙurin sulhunta ɓarakar siyasar jihar dafa ɓangaren Gwamnatin Tarayya.

Ministan ya ce, Shugaba Bola Tinubu ya gana da jiga-jigan ‘yan siyasar jihar ciki har da gwamnan da Wiken kansa, a wani yunƙuri na ɗinke ɓarakar da ke shirin kunno kai a tsakaninsu.

By Babaji