Gwamnatin Kano ta nemi ta tarayya ta hana Kwankwaso shiga Kano, inji Buba Galadima

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Jigo a jam’iyyar NNPP, Buba Galadima, ya yi zargin cewa Gwamnatin Jihar Kano ta rubuta saƙo zuwa ga Gwamnatin Tarayya da ke neman a hana Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso shiga jihar.

Buba Galadima ya bayyana hakan ne a wata hira da manema labarai ranar Alhamis, inda ya ce suna da masaniya akan yunƙurin da ake yi, amma har yanzu suna jiran martanin hukumomin tarayya.

A cewarsa, “Mun samu labarin cewa an rubuta wasiƙa domin hana Kwankwaso shiga Kano. Amma mu na jira mu ga abin da Gwamnatin Tarayya za ta ce.”

Ya kuma yi tambaya akan ko akwai yunƙurin maimaita abin da ya ce an taɓa yi a baya, yana mai cewa za su ƙalubalanci duk wani mataki a gaban kotu idan har an ɗauke shi.

Haka kuma ya yi tsokaci akan rahotannin da ke cewa ana shirin ƙaƙaba wa Kwankwaso takunkumin biza daga Amurka bisa zargin tauye ’yancin Kiristoci, inda ya yi watsi da zarge-zargen da cewa siyasa ce kawai ake yi.

Kazalika, ya ƙara da cewa barazanar ba ta ba su mamaki ba, domin akwai yunƙurin matsin lamba na tilasta wa Kwankwaso shiga jam’iyyar APC.

A ƙarshe, Galadima ya jaddada cewa Kwankwaso ba zai sauya matsayinsa ba, yana mai bayyana shi a matsayin jarumi mai tsayin daka wanda ba ya jin tsoron matsi daga ɓangaren adawa.

By Babaji