
Daga RABI’U SANUSI a Kano
Gwamnatin Jihar Kano ta sake jaddada aniyarta ta bai wa aikin tattara bayanai na ƙasa da Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa (NBS) ke gudanarwa cikakken goyon baya, tana mai bayyana muhimmancinsa wajen tsara ci-gaba mai ɗorewa da inganta rayuwar al’umma.
Da yake karbar bakuncin tawagar NBS tare da wakilan UNICEF da Bankin Duniya a Fadar Gwamnatin Kano, Shugaban Ma’aikatan Fadar Gwamnati, Dr. Sulaiman Sani Wali, mni, wanda ya wakilci Gwamna Abba Kabir Yusuf ya tabbatar da cewa gwamnatin jihar za ta bada dukkan hadin kan da ake bukata domin ganin an samu nasarar aikin.
Dr. Wali ya bayyana cewa, ko da yake Gwamna Yusuf ya yi niyyar karbar tawagar da kansa, wasu muhimman ayyuka na gwamnati ne suka hana shi samun damar halarta.
Shugaban Ma’aikatan fadar Gwamnatin ya jaddada cewa sahihan bayanai su ne ginshikin tsare-tsare masu inganci da ci gaban al’umma, yana mai cewa gwamnatin jihar za ta samar da dukkanin hanyoyin da suka dace domin tabbatar da nasarar aikin.
Haka kuma ya bayyana cewa hadin gwiwar da ke tsakanin Jihar Kano da Hukumar Kididdiga ta Kasa ba ta takaitu ga wannan aiki kadai ba,domin za ta ci gaba da taimakawa wajen tsara manufofi da aiwatar da ayyukan ci gaba a fannoni daban-daban.
Ya kuma kara da cewa kudurin Gwamna Abba Kabir Yusuf shi ne samar da cikakken goyon baya domin tabbatar da nasarar wannan aiki, wanda zai amfanar da al’ummar Kano da kasa baki daya.
Tun a jawabin sa da Farko Shugaban Hukumar Kididdiga ta Kasa, Prince Yemi Adeniran, ya yaba da irin kokarin da Gwamnatin Kano ke yi wajen bunkasa ci gaba da inganta shugabanci a jihar.
Prince Yemi ya bayyana cewa matakan da gwamnatin jihar ke dauka a muhimman fannoni, musamman kiwon lafiya da samar da ingantattun ayyukan jama’a, na nuna jajircewa da hangen nesa wajen kyautata rayuwar al’umma.
A cewarsa, irin wadannan nasarori na sanya Kano cikin jihohin da za su fi cin gajiyar shirye-shiryen gwamnatin tarayya, musamman ta fuskar tsare-tsare da suka dogara da bayanai.
Prince Adeniran ya kuma nuna gamsuwarsa da yadda jihar ke inganta ababen more rayuwa da tsaro, yana mai bayyana Kano a matsayin jiha mai ci gaba da daukar matakan da suka dace domin samar da yanayin da zai taimaka wajen cigaba da walwalar al’umma.
