Ƙungiyar Kiristoci a Kano ta ziyarci tsohon ɗan takarar gwamna na ADC

Spread the love

Daga RABI’U SANUSI a Kano

‎Wasu jagororin Kiristoci daga yankin Kudu maso Yammacin Jihar Kano sun kai ziyarar girmamawa ga tsohon ɗan takarar gwamnan Kano a ƙarƙashin Jam’iyyar ADC, Malam Ibrahim Khalil, domin tattaunawa akan haɗin kai da ci-gaban al’umma.

‎Da yake jawabi a madadin tawagar da sauran mambobin jam’iyyar, Fasto Shehu Maikyau ya bayyana cewa ziyarar ta samo asali ne daga bukatar kara karfafa zaman tattaunawa da hadin gwiwa, musamman wajen lalubo hanyoyin ci gaba.

‎Ya ce, sun ga dacewar ADC a matsayin jam’iyya mai bai wa kowa damar bayyana ra’ayinsa ba tare da tsangwama ba.

‎Faston ya ƙara da cewa, kwarewar da suka samu a siyasar baya ta sa suka zama masu taka-tsantsan, amma suna da yakinin cewa tafiyar siyasar Malam Ibrahim Khalil za ta haifar da alheri da sauyi mai anfani ga al’umma.

‎Tawagar ta yi alƙawarin bada cikakken goyon baya domin ganin an samu nasara a kokarin da zai kawo saukin rayuwa ga jama’ar Jihar Kano da kasa baki daya.

‎A nasa jawabin, Malam Ibrahim Khalil, wanda ya tsaya takarar gwamna a zaben 2023 ƙarƙashin ADC, ya ce daga cikin manyan ƙalubalen da ke gaban al’umma akwai son zuciya da jahilci.

‎Ya bayyana cewa, matsalolin da jama’a ke fuskanta a yau sun samo asali ne daga rarrabuwar kai da ake haddasawa a tsakanin su.

‎Ya jaddada cewa ko dan siyasa ko wanda ba dan siyasa ba, kowa na bukatar hadin kan juna domin cimma ci gaba mai dorewa.

A cewarsa, babban burin tafiyarsu shi ne gina haɗin kai da ƙarfafa zumunci a tsakanin jama’a.

‎“Duk wanda ke rayuwa a doron kasa Allah Ya halicce shi da wata manufa, babu wanda aka halitta babu amfani,” in ji shi. “Ya zama wajibi mu fahimci rayuwa ta hanyar da za ta samar da zaman lafiya da taimakon juna.”

‎Shi ma Mataimakin Sakataren Jam’iyyar ADC a Kano, Shehu Muhammad, ya bayyana Malam Ibrahim Khalil a matsayin mutum mai rungumar kowa ba tare da la’akari da addini ko bambanci ba.

‎Ya ce, suna da yaƙinin cewa wannan tafiya ta siyasa mai albarka ce wadda ta dace da manufofin jam’iyyar.

‎An gabatar da tawagar ne ga tsohon dan takarar gwamnan ta hannun Hon. Haruna Yahaya Kadana, shugaban ‘yan takarar ADC a Jihar Kano.

By Babaji