
A ranar Laraba jami’an Hukumar Zaɓe na Ƙaramar Hukumar Bichi da ke Jihar Kano za su kammala yi wa al’ummar yankin Mazaɓar Yallami rijistar katin zaɓe.
Saidai a wannan mazaɓa jami’an hukumar a yankin sun samu tangarda wajen gudanar da ayyukansu sakamakon kalubalen rashin karfin netwok da yake addabar yankin a mafi yawan lokutan gudanar da ayyuka da ake aiwatarwa ta onlayin makamantan irin wannan.
Amma, duk da haka, Baturen zaɓe na Bichi, Alhaji Abdur-Rahman Haruna Rafin-Dadi ya tabbatar daga fara aikin rijistar a yankin zuwa yanzu sun cim ma nasarar yi wa kaso tamanin cikin dari na al’umar dake Mazabar Yallamin.
A yayin da suka gano wani sashe da akan samu netwok jefa-jefa a yankin, inda aka sanar da kafatanin jama’ar Mazaɓar Yallamin zuwa wannan waje domin a samu damar yi wa kowa rijistar zaben yadda yakamata.
Kazalika ya tabbatar da cim ma nasarar kammala aikin rijistar ga wadanda suka rage na wannan mazaba a yau rana ta karshe.
Haka kuma, duba da tunasarwa, Baturen Zabe na yankin ya yi kira ga daukacin al’umar Karamar Hukumar Bichi.
“Yakamata mutane su tabbatar da cewa, sau daya ake yin rijistar zabe, duk wanda ya zo yi aka tambaye shi ya yi rijistar zabe? Idan har ya tabbatar ya yi to ya fadi gaskiya cewa ya yi, domin yin rijstar sau biyu akwai matsala saboda mai yuwuwa ne a goge sunan mutum ko kuma kwamfuta ta gane ya taba yi, abu ya zama matsala ya zamana cewa sunan mutum ya goge gaba daya. Don haka, muna kira ga mutane su kiyaye da wannan, idan kuma wani gyara ne suke so a yi musu to wannan mutane suna da dama ba zai shafi ainahin rijistarsu da suka yi ba, kawai gyare ne”, Inji Haruna Rafin-Dadi.
A ƙarshew, a wannan matsaya ana sanar da dukkan jama’ar Mazabar Waire da su zama cikin shiri daga gobe Alhamis sha biyu ga watan Fabrairu na wannan shekara da ake ciki 12/2/2026 za a fara yi musu rijistar zabe, inda za a kammala da su a ranar Talata sha bakwai ga wannan watan na Fabrairu 17/2/2026, da fatan al’umar yankin za su ba da hadin kai domin samun nasarar aikin yadda ya dace.




