An bankaɗo yadda Kotun Ƙoli ta yi sama-da-faɗi da Naira biliyan 12 lokacin mulkin Buhari

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Rahoton bin diddigin ayyuka da aika-aikar da aka tafka a Kotun Ƙoli, wanda Ofishin Akanta Janar na Ƙasa ya fitar, ya bayyana cewa an yi ba daidai ba wajen kashe Naira biliyan 12, tsawon shekaru biyar a kotun.

Ofishin Akanta Janar ya ce Kotun Ƙoli ba ta kashe kuɗaɗen ba bisa ƙa’ida ba, don haka a gaggauta maida su asusun gwamnatin tarayya.

Rahoton ya umarci Babban Rajistara na Kotun Ƙoli cewa ya maida kuɗaɗen aljihun gwamnati da gaggawa.

An dai fitar da rahoton tun cikin watan Disamba, kuma ya faɗo hannun Blueprint Manhaja, ta dafe.

Rahoton ya ƙunshi binciken yadda ma’aikatu da hukumomi da cibiyoyin gwamnatin tarayya suka kashe kuɗaɗen su a cikin 2020. Amma a binciken kan Kotun Ƙoli, sai aka faɗaɗa har shekaru huɗu kafin 2020, ya zama shekaru biyar kenan.

An bi diddigin yadda aka kashe kuɗaɗe a kotun, tun daga 2017 har zuwa 2021.

To sai dai kuma Babbar Rajistara ta Kotun Ƙoli da ke kan muƙami a yanzu, ita an naɗa ta ne cikin 2021, shekara ɗaya bayan an yi ƙoƙarin kashe kuɗaɗen ba bisa ƙa’ida ba.

Lamarin ya faru ne tun lokacin Hadizatu Uwani-Mustapha ke Babbar Rajistara ta Kotun Ƙoli.

Uwani ta yi ritaya cikin watan Yuni, 2021. A tsawon lokutan shekaru biyar ɗin da aka kashe kuɗaɗen, Walter Onnoghen ne Babban Jojin Nijeriya daga 2016 zuwa 2019. Sai kuma Tanko Muhammad daga 2019 zuwa 2022.

Tanko Muhammad ya sauka ya yi murabus cikin Yuni 2022, inda ya bada dalili na rashin lafiya, yayin da manyan alƙalan Kotun Ƙoli suka matsa masa lamba da hargagi da bore kan yadda ya ke tu’ammali da kuɗaɗen Kotun QƘoli da sauran al’amuran kotun a lokacinsa.

Daga cikin abin da rahoton ke zargi, akwai kashe kuɗaɗe ba tare da bin turbar kasafin kuɗi ba. Kashe kuɗaɗe a kan abubuwan da ba su cikin kasafin kuɗi, karkatar da kadarorin gwamnati zuwa amfanin kai, ƙara toliyar kuɗaɗe kan adadin kuɗaɗen kwangila, bayar da kwangiloli ba bisa ƙa’ida ba, aringizon biyan ‘yan kwangila fiye da haƙƙinsu da sauransu.

By Editor