An biya sadakin N20,000 ga jikar David Mark domin ƙarfafa wa matasa

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

An biya N20,000 ga iyalan Honarabul Blessing Onuh da ke wakiltar mazaɓar Otukpo/Ohimini a jihar Benuwe a matsayin sadakin auren ɗiyarta.

Honarabul Onuh ɗiyar ce ga tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata David Mark.

Adadin kuɗin ya zama sadakin auren jikar Mark kuma iyalan Farfesa Bishop Obeka Sunday, mataimakin shugaban jami’ar Wesley, jihar Ondo ne suka biya.

Farfesa Sunday shi ne mahaifin Caleb Obeka, wanda ya auri Margaret Onuh bisa ga al’ada. Kuma ma’auratan su na da digiri na PhD.

Basaraken gargajiya, Ochi Otukpo, Dokta John Eyimonye ne ya jagoranci ɗaurin auren, inda ya bayyana cewa Allah ne ya ƙaddara auren. Ya bayar da shawarar a rage farashin sadakin domin ƙarfafa wa matasa gwiwa wajen yin aure, tare da bayyana cewa babban abin da ya shafi auratayya shi ne samun albarkar Ubangiji.

Dokta Eyimonye ya gode wa iyalan Onuh da suka amince da sadakin amaryar, inda ya ce muhimmancin shi ne na ba da misali mai kyau ga wasu.

Da yake jawabi a madadin iyalan Onuh, Mista Ahubi Jonathan ya bayyana cewa bai kamata sadaki amaryar ya yi yawa ba, ya ƙara da cewa ma’auratan su na buƙatar tallafi don samun ci gaba a rayuwar aurensu da kuma rayuwa cikin jin daɗi.

Ya ce ya kamata a daina kashe maƙudan kuɗi a wajen sadaki a ƙasar Idoma domin ƙarfafa gwiwar matasa su yi aure.

Farfesa Sunday ya nuna godiya ga Hon. Iyalan Onuh saboda fahimtarsu wajen karɓar sadakin amaryar.

By ukarofi