Ambaliya: Ba a saki madatsar ruwan Lagdo ba – Gwamnatin Nijeriya

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Ma’aikatar Albarkatun Ruwa da Tsaftar Muhalli ta Tarayya ta bayyana cewa hukumomin ƙasar Kamaru ba su saki ruwa daga madatsar ruwan Lagdo ba, saɓanin jita-jitar da ake yaɗawa a kafafen yaɗa labarai.

A wata sanarwa da Babban Sakataren Ma’aikatar, Richard Pheelangwah ya raba wa manema labarai, ya ce Minista Injiniya Farfesa Joseph Terlumun Utsev a ranar 7 ga watan Yulin 2025 ya yi tattaunawa kai tsaye da manajan madatsar ruwa na Lagdo Ahmad Bivong, wanda ya tabbatar da cewa madatsar ruwa a halin yanzu ba ta kai mita 2.06 ba kuma ba a samu ambaliya ba.

Ya ce, a halin yanzu ma’aikatar tana ci gaba da tattaunawa da hukumomin Kamaru tare da tabbatar wa jama’a cewa duk wani saƙo da aka fitar a hukumance za a sanar da shi cikin gaggawa.

Ya buƙaci jama’a da su yi watsi da rahotannin ƙarya kuma su kwantar da hankula yayin da suke ci gaba da kiyaye matakan ambaliyar ruwa da tsare-tsare da aka fitar a baya

Ministan ya kuma shawarci al’ummomin da ke karɓar saƙonnin gargaɗin gaggawa, musamman Lokoja (jihar kogi) Wurobokki (jihar Adamawa) da kuma Makurdi (jihar Benue) da su kiyaye saƙonnin gargaɗin da wuri tare da tuntuɓar hukumar NIHSA don samun ingantattun bayanai na zamani.

“Bugu da ƙari, ana amfani da madatsar ruwa ta Kashimbila da ke jihar Taraba domin shawo kan ambaliyar ruwa, yayin da inganta tsarin nazarin madatsar ruwa ta Dura a jihar Benuwe ya kai wani mataki na ci gaba,” inji shi.

By ukarofi