Kwastom ta kama maƙudan kuɗaɗen waje a filin jirgin saman Kano

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Hukumar Kwastom ta Nijeriya (NCS) shiyar Jihar Kano da Jigawa, ta kama wasu kuɗaɗen ƙasashen waje, sama da Naira Miliyan 600, tare da kama wasu mutane uku da ake zargi a filin jirgin saman Mallam Aminu Kano (MAKIA).

Hukumar ta bayyana hakan ne a ranar Talata yayin wani taron manema labarai tare da haɗin gwiwa da Kwanturolan Rundunar Kano/Jigawa, Dalhatu Abubakar, da Daraktan Shiyya na Hukumar EFCC na Kano, Ibrahim Shazali suka yi.

Abubakar ya bayyana cewa an kama waɗanda ake zargin ne da wasu kuɗaɗen ƙasashen waje da aka boye a cikin jakunkuna. Daya daga cikinsu mai suna Ahmed Salisu, wanda yake da fasfo na ƙasar Ghana mai lamba G5347658 ya isa Nujeriya daga ƙasar Saudiyya a cikin jirgin ƙasar Habasha da misalin ƙarfe 12:15 na rana a ranar 7 ga Yuli, 2025.

Ya bayyana cewa jami’an hukumar ne suka kama waɗanda ake zargin da kuɗaɗen ƙasashen waje waɗanda suka tattara sahihan bayanan sirri tare da haɗin gwiwar wasu hukumomi a ciki da wajen ƙasar.

Ya ƙara da cewa, da isowar wanda ake zargin kamar sauran fasinjojin, an tuna masa da wajibcinsa na bayyana duk wani kuɗin waje ko kayan aiki da ya wuce dala 10,000, amma ya ƙi yin hakan.

Abubakar ya ce, bisa ga bayanan sirri, an tsare wanda ake zargin don ci gaba da bincike.

A yayin binciken jami’an sun gano wasu kuɗaɗe na ƙasashen waje da aka ɓoye a cikin kwalayen tufafi, da aka kiyasta adadin kuɗaɗen da aka kama sun kai N653,987,268.50.

Ya bayyana ɓoyewar a matsayin wani yunƙuri na kaucewa ganowa, yana mai jaddada cewa, rundunar za ta ci gaba da jajircewa don kama masu aikata laifukan fasa kwauri.

Ya kuma ƙara da cewa, rundunar tare da haɗin gwiwar EFCC sun fara gudanar da cikakken bincike kan lamarin kafin a gurfanar da su a gaban kotu.

Daraktan shiyya na hukumar EFCC, Ibrahim Shazali, ya yaɓa wa hukumar kwastom ta Nijeriya bisa nasarar gudanar da aikin da ya dace.

Da yake magana a madadin Shugaban Hukumar EFCC, Ola Olukoyede, Shazali ya bayyana matukar jin daɗin hadin gwiwar da hukumomin biyu ke yi.

Ya ce aikin na haɗin gwiwa ya nuna aniyarsu ta tabbatar da tsaron iyakokin Nijeriya da yaki da laifukan rusa tattalin arziki

A cewarsa, aikin da aka yi a ranar 7 ga watan Yuli a filin jirgin sama na Mallam Aminu Kano ya biyo bayan samun sahihan bayanan sirri da kuma gudanar da bincike mai zurfi.

By ukarofi