An cafke ɗan sanda yana yunƙurin safarar alburusai zuwa Nasarawa

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

An kama wani Sufeton ’Yan Sanda a Abuja da laifin yunƙurin safarar buhunan alburusai a tashar mota ta Nyanya.

Majiyoyin tsaro sun bayyana cewa da misalin ƙarfe 3:15 na rana. A ranar 19 ga Afrilu, jami’an da ke aiki tare da ‘yan ƙungiyar tashar mota ta Keffi sun fara zargin wani ƙunshin da aka yi niyyar kaiwa zuwa Lafia, babban birnin jihar Nasarawa.

A wani bincike da aka gudanar a cikin ƙunshin an gano wata gidan alburushin AK-47 ɗauke da harsashi guda 30.

Wanda ake zargin, a cewar Zagazola, mai suna Insfekta Kasimu Usman, yana aiki ne a sashin kawar da bama-bamai (EOD) na rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya. Nan take aka kama shi aka tsare shi.

A yayin da ake yi masa tambayoyi, Usman ya amsa cewa ƙunshin an ɗauke shi ne don wani ɗan sanda mai suna Insifekta Haruna Mohammed da ke aiki da rundunar ‘yan sanda ta 58 (PMF) a jihar Nasarawa.

Sufeto Usman na tsare yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike kan yadda ya ɗauko harsashin soja ba tare da izini ba.

By ukarofi