Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Gwamnatin Nijeriya ƙarƙashin jagorancin Bola Ahmed Tinubu na shirin cire layin lantarkin fadar shugaban ƙasa na Aso Rock daga babban layin wutar lantarki na ƙasa saboda tsadar wutar lantarki yayin da ta amince da kasafin kuɗin Naira Biliyan 10 don kafa na’urar samar da wutar lantarki mai amfani da hasken rana.
Rahoton da ya fito daga jaridar The PUNCH ya bayyana cewa, hakan ya biyo bayan ƙarin kasafin kuɗin da aka yi wa fadar gwamnatin tarayya, wanda ya tashi daga biliyan N47.11 a kasafin kuɗin shekarar 2025 da aka fara gabatar da shi zuwa biliyan N57.11 a sigar da aka amince da ita.
Takaddar ta nuna cewa an samu ƙarin kuɗin ne saboda shirin da aka yi na aikin na’urar samar da wutar lantarki mai amfani da hasken rana, mai taken “Solarisation of the ɓilla with Solar Mini Grid,” tare da cikakken kason biliyan N10.
Matakin na zuwa ne a daidai lokacin da ake ƙara nuna damuwa kan rashin dogaro da wutar lantarki ga jama’a da kuma tsadar wutar lantarki ga gidaje da cibiyoyin gwamnati.
Ana sa ran aikin samar da na’urar zai rage dogaro ga tsarin samar da wutar lantarki na ƙasa tare da taƙaita tasirin ƙarin kuɗin fiton kan kuɗaɗen gwamnati.
Ya kamata a lura cewa tun farkon 2024, farashin wutar lantarki ya ci gaba da hauhawa, musamman ga masu amfani da rukunin Band A, waɗanda ke samun aƙalla sa’o’i 20 na wutar lantarki a kullum.
A cikin Afrilu 2024, jadawalin kuɗin fito na masu amfani da Band A ya haura daga N68/kWh zuwa N225/kWh, wanda ke wakiltar ƙarin sama da kashi 230 cikin ɗari.
Duk da cewa daga baya aka daidaita wannan zuwa N206.8/kWh sannan kaɗan zuwa N209.5/kWh a watan Yuli, ya kasance ɗaya daga cikin mafi girman farashin lantarki a ƙasar.
