Daga AISHA ASAS
A ranar Talata. wani alƙali ya bayyana yunƙurin da gwamnatin Donald Trump na Amurka ke yi na rufe kafar rediyon Muryar Amurka (ɓOA) a matsayin abinda ya saɓa wa ƙa’ida, kafin ya bayar da umurnin dakata rufe kafar ta yaɗa labarai wadda ke samun tallafin gwamnatin Amurka.
Alkalin Kotun Amurka, Mai Shari’a Royce Lamberth, ya umurci cibiyar gidan rediyon Muryar Amurka, Hukumar Kula da Kafafan Yaɗa Labarai ta Amurka (USAGM), da ta mayar da Muryar Amurka da sauran kafafen yaɗa labarai a ƙarƙashin inuwar USAGM tare da haramtawa hukumar hana su aiki a matsayin majiyoyin labarai masu dogaro da kai, kamar yadda doka ta tanada.
Ya kuma umurci hukumar ta USAGM da ta maido da aikin yi ga ma’aikatanta da aka ba su hutu kuma kada ta rage yawan ma’aikatanta yayin da ake ci gaba da shari’a, baya ga ci gaba da bayar da kuɗaɗe don watsa shirye-shiryen ƙasa da ƙasa.
“A takaice dai, waɗanda ake tuhuma ba su da wata hujja ta dubawa don rufe USAGM da wannan Kotun za ta iya ganewa,” inji Lamberth, wanda aka naɗa a zamanin tsohon shugaban ƙasa Reagan.
“Sun ɗauki matakin gaggawa don kashe USAGM, ba tare da la’akari da ayyukan da ake buƙata na doka ko tsarin mulki kamar yadda harshen EO ya buƙata ba, kuma ba tare da la’akari da cutar da ma’aikata, ‘yan kwangila,’ yan jarida, da masu amfani da kafofin watsa labaru na duniya ba.
“Yana da wuya a iya fahimtar nunin kai tsaye na ayyuka na son zuciya fiye da ayyukan waɗanda ake tuhuma a nan.”
Wasu daga cikin ‘yan jarida na Muryar Amurka, ƙungiyoyin sa-kai na ‘yan jaridu na duniya masu fafutuka, ‘yan jarudu masu zaman kansu na ‘Reporters Without Borders’ ne suka kai ƙarar gwamnatin Trump a watan da ya gabata sakamakon yunƙurin da ya yi na wargaza harkar aikin jarida.
Bayan Trump ya ba da umarnin rufe USAGM, an sanya ma’aikatanta da ‘yan kwangilar hutun dole. Gamayyar ƙungiyar da ta kai ƙarar ta kuma nemi a maido da kuɗaɗen da ake bai wa ‘yan uwanta na Muryar Amurka da suka haɗa da Rediyo Free Europe/Radio Liberty (RFE/RL), Radio Free Asia, Middle East Broadcast Network da kuma Open Technology Fund.
Sai dai, Lamberth ya ce umarnin nasa bai shafi RFE/RL ko Open Technology Fund ba.
Lauyoyin gamayyar sun yi muhawara a ranar Alhamis yayin sauraron ƙarar farko ta Muryar Amurka cewa, “yin shiru” ya hana duniya samun ingantattun labaran da majalisar ta yi alƙawarim samarwa a lokacin da ta kafa cibiyar sadarwar. Duk da umarnin da Shugaba Trump ya bayar na nuni da cewa kafar sadarwar “ba ta da amfani” sai dai yin shiru da ta yi na lalata muradun Amurka a ketare, inji su.
Andrew Celli, ɗaya daga cikin lauyoyin, ya ce rashin jituwar da ke tsakanin gwamnatin da cibiyoyin sadarwa na USAGM ya samo asali ne daga rahotannin da suka bayar game da rahoton da ta yi kan Hamas ko kuma ‘yancin mata-maza da ke nuni da tsaurarawar da Trump ya yi.
