Daga BASHIR ISAH
Hukumar Karɓar Ƙorafe-ƙorafen Jama’a da Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Kano, ta kama tare da tsare Kwamishinan Ayyuka da Samar da Ababen More Rayuwa na tsohuwar gwamnatin Ganduje, Idris Wada Saleh.
Majiyarmu ta ce an tsare tsohon kwamishinan ne tare da wasu mutane biyar bisa zargin almundahanar Naira biliyan ɗaya.
Majiyar ta ce Babban Sakataren Hukumar Kula da Harkokin Gwamnati, Mustapha Madaki Huguma da Daraktan Kuɗi da na Bincike da Tsare-tsare, na daga cikin waɗanda kamen ya shafa da yammacin Litinin.
Ana zargin waɗanda lamarin ya shafa ne da yin kwanciyar kaza kan Naira biliyan 1 da aka ware don ayyukan hanyoyi da magudanan ruwa guda 30 wanda ba a kammala ba.
Bayanai sun ce kuɗin wanda aka cire daga asusun banki har sau uku a lokuta mabambanta, an tura ma wasu kamfanoni uku a Afrilun 2023.
Majiyar jaridar Daily Post ta ce, kamfanonin da aka tura wa kuɗin na bogi ne wanda babu ɗaya daga cikinsu mai ofishi takamamme.
Majiyar ta ƙara da cewa,
“Ofishin A-bi-ƙa’ida ya ce an ba da takardar amincewa da gudanar da aikin ne saboda Hukumar Kula da Hanyoyin ta ce za a yi aikin gyaran hanyoyin ne ta hanyar amfani da ma’aikatan cikin gida, amma kuma takardun da aka miƙa na nuna abu daban.”
Mai magana da yawun hukumar, Abba Kabir, ya tabbatar da tsare waɗanda lamarin ya shafa, tare da cewa za a gurfanar da su a kotu da zarar an kammala bincike.