Rahoton EU: Atiku da Obi sun yi ca a kan Tinubu

Daga BASHIR ISAH

‘Yan takarar shugaban ƙasa, Atiku Abubakar na Jam’iyyar PDP da Peter Obi na Jam’iyyar Labour a zaɓen 2023 da ya gabata, sun yi ca a kan Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, na ƙin yarda da rahoton ƙarshe da Ƙungiyar Tarayyar Turai (EU) ta fitar kan zaɓen shugaban ƙasa da ya gudana a ranar 25 ga Fabrairun da ya gabata.

A ranar Talata, 27 ga Yuni, EU ta miƙa rahoton nata game da zaɓen a Abuja.

Babban jami’in sanya ido, Barry Andrews, ya ce rahoton ya samo asali ne daga nazarin bin ƙa’idojin da Nijeriya ta ɗauka na shiyya-shiyya da na ƙasa da ƙasa na zaɓukan dimokuraɗiyya.

Andrews ya ga gazawar hukumar zaɓe INEC, la’akari da yadda aka fuskanci matsaloli na rashin ingancin na’urar BAVAS da kuma shafin duba sakamakon zaɓen a intanet.

Wanda a cewarsa hakan ya haifar wa ‘yan ƙasa da sanyin gwiwa game da zaɓen.

Sai dai, a martanin da ta mayar kan rahoton, Gwamnatin Tarayya ta bakin mai bai wa Shugaban Ƙasa Shawara Kan Ayyuka na Musamman, Dele Alake, ta bayyana rashin ingancin rahoton na EU cikin sanarwar da ta fitar a ranar Lahadi.

A nasa martanin kan rajoton, Atiku Abubakar ta bakin mai magana da yawunsa, Mr. Phrank Shaibu, ya yi iƙirarin cewa rahoton na EU kan zaɓen 2023 ya nuna sakamakon zaɓen ba shi ne ainihin abin da ‘yan Nijeriya suka zata ba bayan kaɗa ƙuri’arsu.

Kana ya caccaki Alake da Fadar Shugaban Ƙasa kan yunƙurin da suke yi na nuna rahoton EU a matsayin mara inganci.

A hannu guda, shi ma Peter Obi ta bakin mai magana da yawunsa, Obiora Ifoh, ya bayyana martanin da Gwamnatin Tarayya ta yi kan rahoton a matsayin ‘magani bayan mutuwa”.

Ya ce, “Jam’iyyar Labour tana bayan rahoton da EU ta gabatar kan zaɓen.

“Mun sha nanata cewa an tafka maguɗi a wannan zaɓe don amfanin APC da ɗan takararsu,” in ji Obiora.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *