BIDIYO: Shugabannin tsaro sun ziyarci Tinubu

Daga BASHIR ISAH

Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara Kan Harkar Tsaro (NSA), Nuhu Ribadu, ya jagoranci sabbin shugabannin fannin tsaro haɗa da muƙaddashin Sufeto Janar na ‘Yan Sanda (IGP), zuwa tattaunawa da Shugaba Bola Tinubu a Fadar Villa da ke Abuja a ranar Litinin.

Mahalarta tattaunawar sun haɗa da Babban Hafsan Tsaro, Manjo Janar Christopher Musa; Shugaban Rundumar Sojin Ƙasa, Manjo Janar Taoreed Lagbaja; Shugaban Rundumar Mayaƙa Ruwa Rear Admiral Emmanuel Ogalla da sauransu.

Idan dai ba a manta ba, makonni biyu da suka gabata ne Shugaba Tinubu ya naɗa sabbin shugabannin tsaron.

Ga wani ɓangare na bidiyon ziyarar:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *