An dawo min da karsashina, inji Farouk Lawan bayan samun yafiyar Tinubu

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Tsohon ɗan Majalisar Wakilai, Farouk Lawan ya bayyana bayyana yafiyar shugaban ƙasa da aka masa a matsayin abinda ya dawo masa da karsashinsa da sabunta fata a gare shi cikin harkokin rayuwa da siyasarsa.

Baya ga Lawan, akwai wasu mutane guda 174 da suka samu yafiyar shugaban ƙasa ciki har da ciki har da magabatan Nijeriya da suka haɗa da Herbert Macaulay da tsohon Ministan Abuja, Manjo Janar Mamman Vatsa (mai ritaya).

A shekarar 2012 aka zargi tsohon ɗan majalisar, wanda ya wakilci mazaɓar Ɓagwai/Shanono ta Jihar Kano da neman attajiri Femi Otedola ya ba shi cin hancin Dala miliyan 3, lamarin da ya saɓa wa dokar haramcin karɓar rashawa.

An yi zargin cewa, ya nemi haka ne da nufin cire Kamfaninsa Otedola na Zenon Petroleum and Gas Limited daga sahuh kamfanonin da ake tuhumar su da badaƙalar tallafin mai, wanda lokacin Lawan ne shugaban ƙwarya-ƙwaryan kwamitin majalisar wakilan akan batun.

Cecekuce akan lamarin ya yi ƙamari ne a lokacin da aka ga wani faifan bindiga da ke nuna yadda Lawan ke ciro dami-dami na kuɗaɗe daga riga da hularsa.

Daga bisani Hukumar kula da lamuran hana rashawa da wasu manyan laifuka (ICPC) ta gurfanar da shi akan laifuka bakwai masu alaƙa da cin hanci, inda wata Babbar Kotun Tarayya da ke Apo a Abuja ta yanke masa hukuncin shekara bakwai a gidan yari.

A watan Fabarairun 2022 ne Kotun Ɗaukaka Ƙara ta sake yin hukunci akan lamarin inda ta rage shekarun da aka yanke masa zuwa biyar, lamarin da Kotun Ƙoli ta tabbatar a watan Janairun 2024.

A watan Oktoba, 2024 tsohon ɗan majalisar ya kammala shekaru biyar ɗin da aka ɗiba masa.

Da yake tsokaci akan yafiyar da Shugaba Bola Tinubu ya masa a wata takarda, Lawan ya miƙa godiyarsa a gare shi, inda ya ce hakan wani yanayi na sabuntaasa fata a al’amuran rayuwarsa na nan gaba.

Farouk Lawan, ɗaya ne daga cikin ƴan majalisa da ke bada gudumawa masu ma’ana domin ciyar da Nijeriya gaba, wanda a lokacin ya shahara akan haka a jiharsa da ma ƙasa baki ɗaya.

By Babaji