Muna haɗa hannu da jami’an tsaro don tsaftace harkan ma’adanai a Nasarawa – Margaret Elayo

Spread the love

DAGA JOHN D. WADA a Lafiya

Kwamishiniyar ma’aikatar muhalli da albarkatun ƙasa ta Jihar Nasarawa Sarauniya Margaret Itake Elayo tace zuwa yanzu akwai kyakkyawar alaƙa tsakanin ma’aikatar muhallin da hukumonin tsoron jihar dabandaban a fannin yaƙi da masu harkokin hakar ma’adanai ba bisa ƙa’ida ba a jihar.

Ta sanar da haka ne a jawabin ta a lokacin da take tattauna da manema labarai a ofishin ta dake ma’aikatar a birnin Lafiya fadar gwamnatin jihar ranar Juma’a na mako da ake ciki.

Tace kawo yanzu ma’aikatar da haɗin gwiwar hukumonin tsoron sun daƙile yunƙurin gudanar da ayyukan hakar ma’adanan ta gurɓataccen hanya musamman ta sintiri na musamman a garuruwa da ƙauyuka daban daban a sassan jihar baki ɗaya.

Kwamishiniyar ma’aikatar muhallin da albarkatun ƙasan sarauniya Margaret Elayo ta ƙara da cewa tuni ma’aikatar ta kuma ƙirƙiro da ingantattun shirye-shirye dake cigaba da inganta harkokin tare da sa ido akai-akai musamman akan baƙi dake zuwa daga waje don haƙar ma’adanan da sauran su.

Ta kuma yi amfani da damar inda ta shawarci mazauna yankunan ma’adanan su rika guje wa daɓi’u dake jawo illoli wa muhalli a jihar da suka haɗa da ambaliya da toshe magudanar ruwa da yashewar filayen gonaki da sauran su don cigaba da cin moriyar albarkatun ƙasan jihar.

Kwamishiniyar ta kuma yi amfani da damar inda ta yaba wa gwamnan jihar Injiniya Abdullahi Sule dangane da ƙirƙiro da tsare-tsare da ke cigaba da inganta harkokin ma’adanan tare da haɗin gwiwar sarakunan gargajiya da sauran masu ruwa da tsaki don tabbatar an cigaba da tsabtacce muhallin jihar da kuma harkokin ma’adanan.

Idan ba a manta ba a ‘yan kwanakin nan ne gwmnan jihar ta Nasarawa Injiniya Abdullahi Sule ya amsa wani gayyata na musamman daga shugaban ƙaramar hukumar Kokona a jihar inda shi kuma gwamnan da tawaga daga ma’aikatar muhallin ƙarƙashin jagorancin kwamishiniyar suka ziyarci yankunan Kokonan don gane wa idanun su yanayin harkokin ma’adanan tare da da tabbatar ana gudanar da ayukan cikin tsari da bin dokoki.

By ukarofi