An fara ƙone-ƙone a wasu wuraren zanga-zanga a Kano

Spread the love

Zanga-zangar matsin rayuwa da ake gudanarwa a kano ta rikiɗe a wani sashin da ya janyo an fara ƙone-ƙone.

Rahoton da Blueprint Manhaja ke samu shine, wasu masu zanga-zangar sub fasa ofishin hukumar da ke kula da harkokin sadarwa in da suka ɗauke abubuwa da dama kamar su kujeru, kwamfuta da sauransu wanda daga ƙarshe suka cinna ma ofishin wuta.

Masu zanga-zangar sun kasance matasa ne wanda suka je kofar gidan gwamnatin jihar suna kiran “bamayi”, “canji muke so”

Masu zanga-zangar an hangesu suna tahowa daga sassa daban daban na jihar.

A wani ɓangare kuma, wasu sun fito suna zanga-zangar nuna rashin amincewa da zanga-zangar a kan titi Audu Baƙo da ke kanon.

Haka ma, a wani sashen Zoo road da ke kanon, wasu masu zanga-zangar sunyi yunƙurin fasa shaguna amma jami’an tsaro suka hana su.

By ukarofi