Gwamnan Zamfara ya biya giratuti na aƙalla 7.3 biliyan ga ma’aikatan da su kai ritaya

Spread the love

Gwamna Dauda Lawal ya biya Giratuti na aƙalla naira biliyan 7.3 ga ma’aikatan Zamfara da su kai ritaya.

Idan bamu manta ba, gwamnatin Zamfara ta kafa wani kwamiti a watan Janairu da zai tantance waɗanda a ke bi bashi tsakanin shekarar 2015 zuwa 2024 da kuma ma’aikatan ƙananan hukumomi daga 2012 zuwa 2019.

Wannan ya fito ne daga bakin mai magana da yawun Gwamnan, Sulaiman Bala Idris inda ya bayyana cewa gwamnati ta biya ₦7,345,674,918.42 na giratuti da ba a biya ba tsawon shekaru.

Ya cigaba da bayyana cewa, an yi wannan biyan ne sau bakwai kuma yanzu haka yana tafiya cikin tsari da nasara. Kuma ya bayyana cewa wannan zai cigaba da faruwa domin inganta aikin gwamnati a jihar.

By ukarofi