Da Ɗumi-Ɗumi: Zanga-zangar da ake yi a faɗin ƙasar nan ta samu rashin fitar matasa a Gusau

Spread the love

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Zanga-zangar da ake yi a faɗin ƙasar a yau ta fara gudana a Gusau babban birnin Jihar Zamfara wanda galibin matasa basu fita ba.

Wakilinmu ya ruwaito cewa, masu zanga-zangar sun yi cincirindo ne a kusa da asibitin ƙwararru na Yariman Bakura ɗauke da wasu kwalayen da suka ƙunshi bayanai kamar haka, a mayar da tallafin man fetur, rashin kyakkyawan shugabanci na gari, a cire harajin wutar lantarki, a buɗe kan iyakokinmu da dai sauransu.

Wakilinmu ya lura cewa matasa da yara ‘yan ƙasa da shekaru goma ne suka fito a zanga-zangar wadda aka fara da misalin ƙarfe 8:30 na safe.

Sai dai an jibge jami’an tsaro na haɗin gwiwa a wasu muhimman wurare da suka haɗa da, gidan gwamnati, babbar kasuwar Gusau, babbar tashar mota, masallatai da dai sauransu.

A jiya ne dai gwamnatin jihar ta rufe dukkan makarantun gwamnati saboda zanga-zangar da kuma fargabar tarzoma.

By ukarofi