Ministan Labarai ya umarci ‘yan Nijeriya su haƙura da zanga-zanga

Spread the love

Ministan ƴaɗa Labarai Mohammed Idris ya shawarci ƴan Nijeriya da su sa himma wajen amfani da irin abubuwan alheri shugaba Tinubu ya kawo maimakon bada himma ga zanga-zanga.

Ministan yayi wannan kiran ne a taron manema labarai na duniya a Abuja.
Ya jaddada cewa, shekara guda na Shugaba Tinubu ya zo da abubuwan alheri da ƴan Nijeriya za su mora sosai.

Ya cigaba da cewa, a shekara ɗaya ya ɗora ginshiƙin cigaban tattalin arziki, tsaro da sauran ayyukan more rayuwa.

Yace kar su manta shugaban kwanan nan ya sanya hannu kan dokar sabon mafi ƙarancin albashi, ya bada umarnin bada motocin da ke amfani da CNG domin rage raɗaɗin cire tallafin mai.

Ya cigaba cewa, da nasarar da aka samu a kotu na ƴancin ƙananan hukumomin shima wani cigaba ne da an daɗe a na jiran shi.

By ukarofi