
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI
Aƙalla mutane 19 ne su ka rasa rayukansu a yayin fashewar wani bom da ake zargin mayaƙan Boko Haram ne su ka dasa a wajen cin abinci a ƙauyen Kawuri da ke ƙaramar hukumar Konduga a jihar Borno.
Lamarin, ya auku ne a ranar Laraba, kwanaki bayan da mayaƙan su ka kai hari ofishin ƴan sandan Jakana da ke ƙaramar hukumar inda aka kashe ɗan sanda da wata mata tare da ƙona motocin sintiri guda biyu.
Wani jami’in gwamnati daga ƙauyen, ya ce lamarin ya auku ne da misalin ƙarfe 8:50 na dare inda mutane ke taruwa a wani wajen shan shayi da hira yayin da wasu da dama su ka samu raunuka.
Sai dai, manema labaru sun yi yunƙurin samun jami’in hulɗa da jama’a na ƴan sanda ta waya, DSP Kenneth Daso, domin ƙarin haske game da lamarin wanda hakan bai yiyuwa ba a lokacin haɗa rahoton.
