Daga USMAN KAROFI
Gwamnatin Saudiyya ta sanar da ganin jinjirin watan Ramadan, wanda ke nuni da fara watan azumin Ramadan a ƙasar.
A cewar sanarwar da aka fitar a yau Juma’a, 28 ga Fabrairu, 2025, al’ummar Saudiyya za su fara azumin ranar farko gobe Asabar.
Wannan sanarwa ta fito ne daga shafin Inside The Haramain, wata kafar da ke mayar da hankali kan labarai daga masallatan Harami biyu mafi tsarki a addinin Musulunci.
