Kotun ƙoli ta soke zaɓen ƙananan hukumomi na Ribas

Spread the love

Daga USMAN KAROFI

Kotu ƙoli, a ranar Juma’a, ta bayyana cewa zaɓen ƙananan hukumomin Jihar Ribas da aka gudanar a ranar 5 ga Oktoba, 2024, bai inganta ba.

Wani kwamitin alƙalai biyar ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Jamilu Tukur ta yanke hukuncin cewa gudanar da zaɓen bai da inganci kuma babu sahihancin sa a doka.

A cikin hukuncinta, Kotu Ƙoli ta soke hukuncin Kotun ɗaukaka Ƙara, wacce ta rushe hukuncin kotun farko bisa hujjar rashin hurumin sauraron shari’ar.

A sakamakon haka, Kotun Ƙoli ta dawo da hukuncin babbar kotun tarayya, wanda ke tabbatar da cewa zaɓen bai da inganci.

By ukarofi