Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Wani sabon rahoto ya yi hasashen samun ƙaruwar kashi 38 cikin 100 na masu kamuwa da cutar sankarar mama a duniya nan da shekara ta 2050.
Rahoton na Hukumar Bincike Kan Kansa (IARC), reshe na musamman na Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO), ya kuma yi hasashen mace-mace a kowace shekara daga cutar zai ƙaru da kashi 68 cikin ɗari.
A cikin rahoton da aka buga a Nature Medicine a ranar Litinin, hukumar ta yi gargaɗin cewa za a ci gaba da samun ƙaruwa idan ba a duba halin da ake ciki ba.
Ya ce, idan aka ci gaba da tafiya a halin yanzu, duniya za ta ga sabbin masu kamuwa da cutar sankarar miliyan 3.2 da kuma mutuwar mutane miliyan 1.1 a kowace shekara nan da tsakiyar ƙarni.
Rahoton ya nuna cewa, “Za a ga alƙaluman da ba su dace ba a ƙasashe masu ƙaramin ƙarfi da matsakaicin kuɗin shiga, inda ba a iya gano cutar da wuri,” inji rahoton.
Masaniyar kimiyar IARC kuma mawallafin rahoton, Joanne Kim, ta ce a kowane minti ɗaya, mata huɗu ne ke kamuwa da cutar sankarar mama a duk duniya, kuma mace ɗaya tana mutuwa daga cutar.
Kim ta ce, waɗannan alƙaluma na aara taɓarɓarewa cikin lokaci.
Ta ƙara da cewa “ƙasashe na iya ragewa ko kuma juyar da waɗannan alƙaluma ta hanyar ɗaukar manufofin rigakafin farko, kamar shawarar da WHO ta ba da shawarar ‘mafi kyawun siyayya’ don rigakafin cututtukan da ba sa yaɗuwa, da kuma saka hannun jari kan gano cutar da wuri,” inji ta.
Kim ta ce, sankarar mama ta kasance mafi yawan cutar kansa a tsakanin mata a duniya kuma shi ne na biyu mafi yawan cutar kansa gaba ɗaya.
A cikin 2022 kaɗai, an kiyasta sabbin mutane miliyan 2.3 sun kamu da cutar, inda aka bayar da rahoton mutuwar mutane 670,000.
