Daga GAMBO ISA
Shugaban ƙaramar Hukumar Kwaya Kusar a Jihar Borno, Honorabul Salihu Adamu Yanga ya yaba wa Gwamna Babagana Umara Zulum bisa ayyukan raya ƙasa a jihar.
Adamu Yanga ya bayyana haka ne a cikin makon nan yayin wata tattaunawa da wakilinmu a Abuja, inda ya zayyana wasu daga nasarorin da gwamnan ya samu a fannin jin daɗi da walwalar al’umma ta fuskar kayayyakin more rayuwa, noma, ilimi, kiwon lafiya, gina manyan kasuwanni na zamani da sauransu.
Honorabul Salihu Adamu Yanga ya lissafo nasarorin da suka haɗa da, shirye-shiryen da suka shafi al’ummar jihar kaitsaye, kamar gina manyan kasuwannin zamani da sauran ayyukan bunƙasa ƙasa a ƙananan hukumomi 27 dake faɗin jihar.
Adamu Yanga, ya yaba da yadda gwamnan ke yaƙi da ‘yan ta’adda, inda Gwamna Zulum yake taimaka wa jami’an tsaron CJTF domin yaƙar ‘yan ta’addar Boko Haram a jihar.
Ya ce gwamnan ya yi tasiri ga rayukan marasa galihu a cikin Kwaya Kusar da sauran ƙananan hukumomin jihar inda ya buƙace su da su tallafa wa yawancin shirye-shiryensa.
Honorabul Adamu Yanga ya jinjina wa Gwamna Babagana Umar Zulum ta fuskar haɓaka ilimi, horas da likitoci, malaman aikin jinya da ungozoma da gina makarantu a cibiyoyin kula da lafiya na matakin farko da wuraren bada magani a gundumomi, a cikin ƙananan hukumomi 27, don ingantaccen tsarin kiwon lafiya.
Honorabul Yanga ya buƙaci al’ummar ƙaramar Hukumar Kwaya Kusar da su shiga cikin shirin noma da shirin gwamna inda gwamnati ta samar da kayan amfanin gona don bunƙasa noma.
Ya kuma shawarci matasa da su kasance jakadu na gari a yankin a kodayaushe, inda ya buƙace su da su yi biyayya ga dokokin tsarin mulki da dokokin ƙasa, su guji shan miyagun ƙwayoyi, su riƙa saurare da mutunta dattijai a cikin al’ummarsu ko yankin da ke sana’ar kasuwanci da koyar da sana’o’i domin dogaro da kai.
Kazalika ya shawarci dattawan yankin da su tallafa wa shirye-shiryen gwamnati wajen gina ƙaramar hukumar.
Ya shawarci takwarorinsa shugaban ƙananan hukumomi 27 da su fara gudanar da shirye-shiryen Gwamna Zulum da su kasance masu riƙon amana ga jama’arsu, domin suna sa ran za a kai musu ribar dimokuraɗiyya.
Ya kuma shawarci ma’aikatan ƙaramar hukumar Kwaya Kusar da su sadaukar da lokacinsu wajen aiki tuƙuru, kuma su guji ɓata lokaci wajen aiki, ya kuma buƙaci ma’aikatan lafiya da su guji ɓata lokaci a bakin aiki.
Honorabul Yanga, ya shawarci matasa, dattijai a cikin al’umma, musamman da su yi wa ƙasa addu’a domin ƙarin wanzuwar zaman lafiya da yalwar arziki a cikin watan Ramadan ɗin nan da za a shiga
