Daga MUHAMMADU MUJJITABA a Kano
ɗaya daga cikin jagororin ‘yan ƙungiyar masu sayar da katako a Jihar Kano, Alhaji Bala Ibrahim, ya ce, shugaban haɗaɗɗiyar ƙungiyarsu ta ’yan katako ta Jihar Kano ƙarƙashin shugabancin Alhaji Yusuf Abdullahi Tanko, ya himmatu wajen tabbatar da an haɗa kan dukkanin ‘yan ƙungiyar masu kishin wannan kasuwanci kuma sanin ya makata domin cin amfanin wannan kasuwanci ta fuskar ƙungiyar kamar sauran ƙungiyoyi masu kishin sanar’arsu suke a jihar Kano da ma Nijeriya baki ɗaya.
Alhaji Yusuf ya bayyana haka ne a wajen wani taro da ƙungiyar ta kira na ‘ya’yanta a kasuwar ƙofar Ruwa a ranar Lahadin da ta gabata.
Haka kuma ya ce wannan taro na gaggawa an yi shi ne domin tabbatar da haɗin kai da zaman lafiya a wannan ƙungiya ta masu sayar da katako ta Jihar Kano da ake kira, Timber Seller Kano Branch, ƙarƙashin shugabanci Alhaji Yusuf Abdullahi Tanko, wanda shi ne shugaban riƙo na ƙungiyar masu sayar da katako na Rijiyar Lemo, kuma haɗaɗɗiyyar masu sayar da katako na Jihar Kano bakiɗaya, haɗin kai domin wa wannan kasuwa haɗin kai, cigaba, da kuma samun fahimtar juna a tsakanin masu wannan sana’a a Kano da ƙasa baki ɗaya, daidai da manufar gwamnatin Jihar Kano na haɗa kan al’umma da kawo musu cigaba a kowane fanni na rayuwa, inda kuma ya bunƙaci Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf da ya tallafawa wannan ƙungiya ta ofishin kwamishinan ciniki da masana’antu na Jihar Kano Alhaji Wada Sagagi, ta hanyar haɗin kai da kuma duk wani abun da ƙungiyar ta ke buƙata wajen tabbatar da wanzuwar zaman lafiya da kwaniciyar hankali.
Taron dai ya samu halartar shugabanni da sauran ƙungiyar daga kasuwa ‘yan katako ta Na’ibawa, Rijiyar Lemo, ƙofar Ruwa, da sauran kasuwannin sayar da katako a Jihar Kano, irinsu jami’in hurɗa da jama’a na ƙungiyar Malam Mukaila Ibrahim, Jamilu Ibrahim ma’ajin ƙungiyar, Sunusi Adamu shugaban ƙungiyar na kasuwa katako na Na’ibawa kuma sakataren haɗaɗɗiyar ƙungiyar masu sayar da katako na Jihar Kano, da sauran ‘yan ƙungiyar na Kano.
