Masarautar Singa ta shirya saukar Alƙur’ani don neman sauƙin rayuwa – Wazirin Masarautar

Spread the love

Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano

Masarautar Kasuwar Singa da ke Birnin Kano bisa jagorancin Mai Girma Alhaji Abba Ibrahim, Sarkin Masarautar Singa kuma babban ɗan majalisar a masarautun kasuwanni ƙaramar Hukumar Fagge da ke Jihar Kano a ƙarƙashin shugaba mai girma Hakimin Fagge, Alhaji Mahmud Bayero, ya bayyana cewa, karatun saukar Alƙur’ani maigirma kuma za a cigaba da ikon Allah domin nema wa kasuwar zaman lafiya, ƙaruwar arziƙi da ƙaramar hukumar Fagge da hakimin Fagge da Kano da Nijeriya bakiɗaya. 

Wazirin Sarkin kasuwar masarautar fadar Singa Alhaji Muntari Ahmad Waru ya bayyana haka ne a yammacin Laraba a madadin Sarkin kasuwar Singa Alhaji Isah Abba Ibrahim.

Haka kuma Waziri a madadin Sarkin kasuwar Singa ya bayyana cewa suna ‘yan kasuwa sun ɗauki dukkan wasu mataikai na ganin cewa sauƙi na kayan abinci da sauran kayan masarufi ya tabbata kamar yadda al’umma ke fata da murna na ganin an samu sauƙin rayuwa a Kano da ƙasa bakiɗaya.

A ƙarshe Wazirin masarautar kasuwar Singa ya yaba wa Hakimin Fagge da Sarkin Kano da gwamnatin Kano da sauran masu ruwa tsaki wajen cigaban Kano, inda kuma ya bayyana wannan masarauta na kyakywar alaƙa da masarautun kasuwannin Kano da sauran al’umma musamman kasancewar masarautar kasuwar Singa na da tasiri wajen harkar bunƙasa a Kano da Nijeriya da ma Afirka bakiɗaya.

By ukarofi