Littafin IBB mai cike da cece-kuce

Spread the love

Tsohon shugaban mulkin soji na Nijeriya, Ibrahim Badamasi Babangida ya fitar da sabon littafin tarihin rayuwarsa inda ya fallasa sirruka da dama game da lokuta daban-daban da aka shiga ruɗani a zamanin mulkinsa tsakanin 1985 zuwa 1993.

Littafin mai taken ‘A Journey in Serɓice’ ya haifar da muhawara kan abubuwan da littafin ya ƙunsa da kuma abubuwan da za su iya faruwa in da abubuwan ba su kasance a haka ba – musamman batun soke zaɓen shugaban ƙasa na 1993 da kuma kisan abokin ƙuruciyarsa.

Waɗanne batutuwa ne ‘yan Nijeriya suka jira tsawon shekaru 32 don jin labari daga abin masana? Babban al’amarin shi ne soke zaɓen 12 ga Yuni, 1993. Wannan zaɓe ya nuna wani yanayi mai cike da ruɗani a tarihin Nijeriya. Wannan ne batu mafi girma a littafin, wanda abu ne da ake ganin ya sauya tarihin Nijeriya. Wasu na cewa har yanzu ƙasar ba ta farfaɗo daga illar soke zaɓen shugaban ƙasa na 1993.

A cikin littafin, Babangida, wanda yanzu yake da shekara 83 a duniya, a karon farko ya bayyana da-na-saninsa kan soke zaɓen.

An sa ran zaɓen zai kawo ƙarshen mulkin soji na shekara 10 a wancan lokacin, kuma soke zaɓen ya jefa ƙasar cikin ruɗani.

Yanzu haka an ayyana ranar da aka gudanar da zaɓen – 12 ga watan Yuni – a matsayin ranar dimokuraɗiyya ta ƙasar. Daga baya an tursasa wa Babangida ajiye mulki.

An kama tare da ɗaure mutumin da ake tunanin cewa shi ne ya lashe zaɓen, Moshood Abiola, sannan kuma aka kashe matarsa.

Shugaban Nujeriya na yanzu, Bola Tinubu ya jinjina wa Babangida tare da yaba masa bisa amsa laifin abin da ya faru.

“Abin da ya faru, abin da na sani ne. ƙasar nan na son ganin na nuna nadamata,” kamar yadda Babangida ya rubuta a cikin littafin.

Janar Babangida, wanda aka fi sani da IBB, ya amince a cikin littafin cewa Abiola, wanda ya mutu a 1998, ne ya lashe zaɓen.

Sai dai a daidai lokacin da ake tattara sakamakon zaɓen a shekarar ta 1993, gwamnatin mulkin soji ta wancan lokacin ta dakatar da tattara sakamakon – wani abu da ya janyo zanga-zanga da shiga halin rashin tabbas.

A wancan lokaci, ya kafa hujja da batun sayen ƙuri’a da kuma ƙoƙarin kare ɓangaren shari’a na ƙasar a matsayin hujjar soke zaɓen.

Sauran batutuwan da suka ci gaba da tayra da ƙura sun haɗa da batun juyin mulkin farko na shekarar 1966 ƙarƙashin jagorancin Manjo Kaduna Nzeogwu, wani ɗan ƙabilar Ibo wanda haifaffen Kaduna ne kuma ya gina sana’arsa a Arewa. Janar Babangida ya ƙara da cewa juyin mulkin ba shi da ma’anar ƙabilanci Ibo duk da cewa juyin mulkin ya nuna yadda ake aiwatar da kisan gilla. Wasu ƙarin taƙaddamar sun haɗa da hamɓarar da Janar Muhammadu Buhari da Janar Yakubu Gowon, da kuma kashe abokinsa Mamman ɓatsa a lokacin suna yara kan zargin yunƙurin juyin mulki. Akwai shakkun cewa iyalan shugabannin da suka rasa rayukansu a wannan juyin mulki na farko ko dangin ɓatsa za su amince da ra’ayin IBB. Janar Mamman ɓatsa da Babangida sun taso a tare, sun yi makaranta ɗaya, aji ɗaya kuma sun yi rayuwar soja tare. Kisan da aka yi wa ɓatsa a shekarar 1986 bayan kama shi da laifin kitsa juyin mulki na ɗaya daga cikin abubuwan da suka janyo cece-kuce a lokacin mulkin Babangida.

Littafin na IBB, “Tafiya A Cikin Hidima Wa ƙasa” ya zama jagora da littafin jagora ga shugabanni na yanzu da masu kishin ƙasa, ma’aikatan soji, da ɗalibai masu ƙarfin iko. Yana ba da ƙarin haske game da sarƙaƙƙiyar tsarin mulki, ƙalubalen jagoranci, da sakamakon yanke shawara masu tsauri. Duk da yake ba kowa ba ne zai yarda da batun IBB ko dalilansa na wasu ayyuka ba, littafin ya ba da kyakkyawar fahimta kan juyin siyasar Nijeriya.

Yayin da Nijeriya ke ci gaba da gwajin dimokuraɗiyya, darussa daga zamanin IBB — masu kyau da marasa kyau — sun kasance ginshiƙin jagora ga makomar siyasar ƙasar.

By ukarofi