Wasu masana Ilimin Kimiyyar Kayan Tarihi sun gano wani hakorin ɗan Adam a Jojiya da ke ƙasar Amurka, da ya kai shekaru miliyan 1.8.
Wannan binciken nasu ya tabbatar na mutane farko-farko ne da suka yi rayuwa a nahiyar Turai.
An gano hakorin a kusa da ƙauyen Orozmani mai tazarar kilomita 100 daga Kudu maso Yammacin Tbilisi, babban birnin Jojiya da kuma kusa da Dmanisi.
A garin na Dmanisi ne a ƙarshen shekarar 1990 zuwa farkon 2000, aka gano ƙoƙon kawunan mutane wadanda aka yi hasashen sun kai shekaru miliyon 1.8. a ƙarƙashin ƙasa.
Binciken ya gano cewa, mutanen sun yi rayuwa a shekarun da suka shuɗe bayan sun yi ƙaura daga nahiyar Afrika.
Wani bincike na baya-bayan nan da aka gudanar ya nuna cewa, yankin Kudancin Caucasus mai tuddai da yawa, ya kasance ɗaya daga cikin wuraren da mutanen farko suka fara zama bayan sun bar Afirka.
Shugaban masu binciken Giorgi Bidzinashbili ya ce, suna hasashen haƙorin na ɗaya daga ƙabilar Zezva ko Mzia ne, waɗanda a baya aka gano ƙoƙon kawunansu, wanda ya nuna sun yi rayuwa a baya sama da shekaru miliyon 1.8 a yankin.
Da ya ke magana da manema labarai game da binciken, Ɗalibin Ilmin Kimiyyar Kayan Tarihi, Jack Peart, wanda ya gano haƙorin ya ce, “Abubuwan da ke faruwa ba a wannan waje ba ne kaɗai, inda mutanen da suka bar Afirka shekaru miliyan 1.8 da suka shuɗe.
“Yana tabbatar da cewa Jojiya wuri ne mai muhimmanci ga ilmin ɓurɓushin halittu da kuma labarin ɗan Adam gaba ɗaya.
