Wani jirgin sama ɗauke da fasinjoji ya ɓace ɓat a sararin samaniya ƙasar Costa Rica.
Al’umma dai sun shiga ruɗani, inda suka fara tsammanin lamarin ka iya zama irin na wani fim mai suna ‘Manifest’, wanda jirgin ya ɓace kuma ya bayyana bayan shekara biyar ba tare da fasinjojin jirgin sun canja ko kaɗan ba.
Jirgin wanda ke ɗauke mutum biyar ’yan ƙasar Jamus daga Meziko ya vace ne da qarfe 12.00 na dare (aggogon GMT) kafin wayewar garin Asabar, a cewar Ma’aikatar Tsaro ta Costa Rica.
Ministan Tsaron Costa Rica, Jorge Torres, ya ce, “Mun samu rahoton ɓacewar wani jirgi mai zaman kansa da ya taso daga Meziko zuwa filin jirgin daga yankin Lardin Limon da ke Gabashin Costa Rica.
Ministan tsaron ya ci gaba da cewa, “Jirgin yana ɗauke da Jamuwasa biyar,” a lokacin da ya ɓace.
Ya ce, “Sadarwa da shi ya katse ne daga kusa da turken sadarwa da ke La Barra de Parismina a Costa Rican Caribbean kuma nan ta ke muka ɗauki matakan da suka dace” domin gano inda jirgin ya shige.
Sai dai ya bayyana cewa, rashin kyan yanayi ya sa an dakatar da aikin neman jirgin, amma za a cigaba daga safiyar Asabar.
