An kama ma’aikatan gidan mawaƙi Davido kan rasuwar ɗansa, Ifeanyi

Daga BASHIR ISAH

‘Yan sanda a Legas, sun kama ‘yan aikin gidan shahararren mawaƙin nan, Davido, domin gudanar da bincikin kan matuwar ɗan mawaƙin, Ifeanyi David Junior Adeleke.

Aƙalla ma’aikata takwas ne ke aiki a gidan mawaƙin da ke Tsibirin Banana a Legas.

Idan za a iya tunawa, a ranar Litinin da ta gabata aka ba da sanarwar rasuwar ɗan Davido da ya haifa tare da budurwarsa Chioma.

Bayanai sun ce marigayin mai shekaru uku, ya shiga kwatanniyar wanka da ke gidan ne alhali bai iya ninƙaya ba, kuma hankalin ma’aikatan gidan bai ka kansa ba balle su san halin da yake ciki a lokacin da lamarin ya faru.

Bayan da aka gano yaron ne aka ciro shi aka garzaya da shi asibiti inda aka tabbatar rai ya yi halinsa sakamakon jimawa da ya yi a cikin ruwan.

Mai magana da yawun ‘yan sandan yankin, SP Benjamin Hundeyin, ya tabbatar da kama ma’aikatan don gudanar da bincike kan batun.