An gudanar da taron tattaunawa kan al’adun Sin da Afirka karo na farko

Daga CMG HAUSA

A jiya ne, aka gudanar da taron tattaunawa kan al’adun Sin da Afirka karo na farko mai taken “sa kaimi ga raya al’umma mai kyakkyawar makoma ga Sin da Afirka a sabon zamani ta hanyar mu’amalar al’adun juna”, wanda kwalejin ilmin zamantakewar al’umma ta Sin, da kwalejin nazarin Afirka na ƙasar Sin, da kuma ofishin ƙungiyar AU dake kasar Sin suka ɗauki nauyin shiryawa.

A wajen taron, babban sakataren kwalejin ilmin zamantakewar al’umma na ƙasar Sin Zhao Qi, ya yi nuni da cewa, an gudanar da taron tattaunawar cikin nasara, wanda ya kasance sabon dandalin yin mu’amalar al’adu a tsakanin Sin da Afirka wanda kwalejin nazarin Afirka na ƙasar Sin ta kafa, kana zai sa ƙaimi wajen zurfafa mu’amalar al’adu a tsakanin Sin da Afirka.

Zaunannen wakilin ƙungiyar AU dake ƙasar Sin Rahamtalla M. Osman ya yi jawabi da cewa, a halin yanzu, ana fuskantar matsaloli da dama a duniya, ƙasashe da yankuna suna fuskantar ƙalubale a fannin samun ci gaba, kana an samu bunƙasuwar fasahohin sadarwa da yanar gizo, an ƙara maida hankali ga ikon yin magana kan al’adu.

A halin yanzu, mu’amalar al’adu ta riga ta kasance muhimmiyar hanyar sa ƙaimi ga raya dan Adam, don haka gudanar da taron tattaunawa kan al’adun Sin da Afirka karo na farko ya dace da yanayin da ake ciki. Kwalejin nazarin Afirka na ƙasar Sin da kungiyar AU sun karbi banƙuncin shirya taron tattaunawar, wanda ya dace da buƙatun Sin da Afirka, kana zai sa kaimi ga masanan Sin da Afirka wajen ƙara yin haɗin gwiwa da juna don ba da shawarwari game da yadda za a bunƙasa ƙasashen Afirka.

Masana da wakilan matasa da ‘yan kasuwa da kuma jami’an diplomasiyya na ƙasashen Afirka dake ƙasar Sin da yawansu ya zarce 120 sun halarci taron tattaunawar.

Mai Fassara:Zainab