An kama ɗan bindiga da aka alaƙanta da kisan Sarkin Gobir

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Jami’an Birget ta ɗaya ta rundunar sojojin Nijeriya sun yi nasarar kama babban jagoran ƴan bindiga, Bako Wurgi (alais Baka Na Garba) wanda ake zargin sa da hannu a kisan Sarkin Gobir, Alhaji Isa Mohammed Bawa a Jihar Sakkwato.

An gudanar da atisayen ne a ranar 14 ga watan Disamba da misalin ƙarfe 10 na dare bayan wani rahoton sirri da ya bayyana cewa Wurgi ya na wani asibiti a garin Shinkafi na Jihar Zamfara sakamakon raunuka da ya samu a wani artabu da suka yi da wasu abokan hamayya.

A yayin haka ne wasu ƴan bindiga biyu suka tsere inda jami’an suka yi nasarar kama direban da ya taimaka wajen kai Wurgi zuwa asibitin.

A ranar 9 ga watan Yuli ne aka yi garkuwa da Sarkin Gobir a ƙaramar hukumar Sabon Birni ta Sakkwato inda aka kashe shi a ranar 22 ga watan Agusta bayan rashin cimma matsaya kan kuɗin fansarsa.

Rahotanni sun bayyana cewa Wurgi ya taka rawa sosai a yayin garkuwa da Sarkin da kuma kashe shi.

Kazalika, Wurgi, wanda ɗan fasa-ƙwaurin makamai ne na Ƙasa-da-ƙasa, yana da alaƙar jini da jagoran ƴan bindiga, Bello Turji ta ɓangaren kakansa.

Kama ɗan ta’addar wata gagarumar nasara ce a ƙoƙarin jami’an tsaro wajen magance matsalolin taɓarɓarewar tsaro a Arewa-maso-Yamma da ma Nijeriya baki ɗaya.

By Babaji