Tinubu ya ɗage gabatar da kasafin kuɗin 2025 ga Majalisar Dokoki

Spread the love

An ɗage ranar gabatar da kasafin kuɗin Naira tiriliyan 47.9 na shekarar 2025 da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu zai yi wa haɗaɗɗen zaman Majalisar Tarayya daga ranar Talata, 17 ga Disamba, 2024, zuwa Laraba, 18 ga Disamba, 2024.

Wata majiya mai ƙarfi daga ma’aikatan gudanarwa na Majalisar Tarayya ta tabbatar wa wakilin Blueprint dake Majalisar Dattawa cewa an ɗage gabatar da kasafin kuɗin da kwana ɗaya.

Majiyar ta ce za a fitar da sanarwar a hukumance kan ɗagewar a cikin sa’o’i masu zuwa.

By ukarofi