Jami’an hukumar ICPC sun yi nasara cafke tsohuwar kwamishinan kuɗi kuma akanta janar ta Jihar Kaduna a zamanin tsohon gwamna Elrufa’i Shizzer Joy Nasara Bada a filin jirgin sama na Legas.
Wannan lamarin ya nuni da cewa tabbas har yanzu a na binciken tsohuwar gwamnati ta Elrufa’i a kan zargin karkatar da kuɗaɗen al’umma a zamanin.
Har yanzu babu takamaimai abinda ake tuhumar kwaminshinan da shi, sai dai masu sharhi sun ce kamun na da nasaba da zarge zarge a kan almubazzaranci, zamba da kuma karkatar da dukiyar jihar. Kuma har yanzu hukumar ba ta yi watsi da yiyuwar ƙara cafko wasu daga gwamnatin da ta shuɗe domin bincike.
