Jerin sunayen ‘yan bindiga 13 da sojojin Nijeriya su ka kashe

Spread the love

Arewacin Nijeriya, musamman Arewa maso Yamma na shan fama da tashe-tashen hankula da ya shafi ‘yan bindiga.

Rikicin wannan yankin ya samo asali ne tun shekarar 2011, bayan da wani rikici ya ɓarke tsakanin manoma Hausawa da Fulani makiyaya. Sai dai wannan rikici ya rikiɗe ya zama babban barazana ga tsaro ga jihohin yankunan kamar sh Katsina, Kaduna da Zamfara.

A baya bayan nan ne rundunar sojin Nijeriya ta kashe wani fitaccen ɗan bindiga da ake kira Kachalla Halilu Sububu a wani farmaki da su ka kai masa. Sububu babban ɗan bindiga ne da ya shahara wajen ayyukan ta’addanci a ƙaramar hukumar Anka ta Jihar Zamfara.

Ga jerin sunayen ‘yan bindiga shahararru da rundunar sojan Nijeriya ta kashe

  1. Buharin Daji
  2. Halilu Sububu
  3. Buhari Alhaji Halidu
  4. Dangote
  5. Boderi Isiyaku
  6. Kachalla Ɗan Chaki
  7. Dogo Gudali
  8. Dogo Rabe
  9. Alhaji Auta kachalla Ruga
  10. Rufa’i Maikaji
  11. Ya’u
  12. Alhaji Karki
  13. Yellow

By ukarofi